Connect with us

Labarai

Ku guji tada hankalin al’umma yayin zaɓen ƙananan hukumomi a Kano – Human Right

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta buƙaci al’umma musamman ma Matasa da su kasance masu bin doka da oda tare kuma da gujewa tayar da hankalin jama’a a yayin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin da za ayi a yau Asabar.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar na Ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a safiyar Asabar.

Ya kuma ce bai kamata al’umma su kasance masu taka doka ba, domin bin doka shi ne wayewa.

“Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su bada gudunmawar su yayin zaɓen domin ganin an gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin cikin kwanciyar hankali, “in ji Tasi’u”.

Da yake nasa jawabin daraktan ƙungiyar Kwamared Gambo Madaki, kira ya yi ga dukkanin ƴan ƙungiyar su na ƙananan hukumomin Kano 44, da ku guji sanya kayan ƙungiyar su yayin gudanar da zaɓen kasancewar ba sa cikin masu aikin zaɓen ko kuma sanya ido, domin gujewa fuskantar matsala.

Tuni dai hukumar zaɓe ta jihar Kano Kanseic, ta ce za’a fara kaɗa ƙuri’a ne da misalin ƙarfe takwas na safiyar yau Asabar.

Labarai

Rashin bayar da shawarwari na kawo tsaiko a karatun Ɗaliban Najeriya – Farfesa Abdurrasheed Garba

Published

on

Shugaban jam’i’ar Khalifa Isyaka Rabi’u ta Chairun da ke jihar Kano Farfesa Abdrulrahsheed Garba, ya ce rashin shigar da tsarin jagoranci da bada shawarwari a mafi yawa daga cikin makarantu a Nijeriya, na taimaka wa wajen sanya matasa su gaza hawa kan kyakkyawar turbar da ta dace da su a rayuwar karatun su da ma sauran al’amura daban-daban.

Farfesa Abdrulrahsheed Garba ya bayyana hakan ne a ganawar sa da gidan rediyon Dala FM, yayin wata ziyara ya da ya kawo gidan a yammacin Juma’a 27 ga watan Disamban 2024.

“Tun kusan shekaru hamsin aka sanya jagorancin da bada shawarwarin wato Guiding and Cancelling, a cikin tsarin ilmin ƙasa a Najeriya, sai dai har kawo yanzu da yawa daga cikin gwamnatocin jahohi da ma gwamnatin tarayya sun gaza tabbatar da shi, “in ji shi”.

Farfesa Abdrulrahsheed Garba, ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar iyaye da makarantu su ƙara dagewa akan ƴaƴan, ita kuma gwamnati ta kara samar da ingantattun makarantu, domin ganin rayuwar ɗalibai ta ƙara hawa kan turba mai kyau.

Continue Reading

Labarai

Ƙarancin kayan aiki na bamu matsala wajen kakkaɓe masu faɗan Daba da ƙwacen Waya a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan mai yaki da fadan Daba da ƙwacen Waya da kawar da Shaye-shaye ta Anty Snaching da ke jihar Kano, ta sha alwashin ci gaba da kakkabe bata garin da ke addabar al’umma da fadan Daba a sassan jihar, domin ƙara wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar.

Kwamandan rundunar Inuwa Salisu Sharada, shi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan redivon Dala FM, a ranar Litinin.

Ya ce za su ci gaba da kokari wajen shiga lungu da sako wajen kawar da dukkanin masu kokarin tayar da hankalin al’umma, duk kuwa da ƙalubalen da suke fuskanta.

“Daga cikin ƙalubalen da muke fuskanta akwai ƙarancin motar fita aiki domin mota ɗaya muke da ita, idan jami’an mu za su fita aiki da mutane da yawa sai dai su hau Baburan Adai-dai Sahu, duk hatsarin wuri; akwai mota a gidan gwamnatin Kano muna fatan gwamna zai bamu ita a ciki gaba da aiki, “in ji Inuwa”.

Kazalika Sharada ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar al’umma su ƙara himma wajen ba su hadin kan da ya dace domin ganin sun kara samun dama wajen magance matsalar tsaro musamman ma ta fadace-fadacen Daba, da ta addabi al’umma a sassan jihar Kano.

A cewar sa, “Ƙarancin motocin fita aikin na ba mu matsala domin a wasu lokutan daga wuri mai nisa ake kiran mu don kai ɗauki akan matsalar tsaro, amma rashin wadatattun motocin mukan fuskanci ƙalubale, “in ji shi”.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke a gaba da neman dauki wajen magance matsalar tsaron da ke damun su a sassan jihar, musamman ma a wasu unguwanni da ke ƙwaryar bimin Kano.

Continue Reading

Labarai

Dalilan da suka sa gwamnan Kano ya bai wa Sani Danja muƙami.

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗa fitaccen ɗan fina-finan Hausar nan na Kannywood, Sani Musa Danja, a matsayin mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin matasa da wasanni.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran gwaman jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi 15 ga watan Disamban 2024.

Sunusi, ya kuma ce gwamnan ya amince da naɗin Sani Danja tare da wasu mutane da shugabannin hukumomin da aka sauya wa ma’aikatu da masu bai wa gwamna shawara daban-daban.

Idan dai ba’a manta ba a mako mai ƙarewa ne dai gwamnan jihar Kano ya yi wa majalisar zartarwarsa garambawul, inda ya sauke wasu ƙusoshin gwamnatinsa, daga ciki kuwa har da sauke sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Baffa Bichi, da shugaban ma’aikatar fadar gwamnatinsa Shehu Wada Sagagi.

Har ila yau, a makon dai gwamnan ya sauke kwamishinan yaɗa labaransa Baba Halilu Ɗan Tiye, da wasu Kwamishinoninsa, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Kafar yaɗa labarai ta Dala FM Kano, ta rawaito cewar, Sani Danja, dai na daga cikin ƴan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Nassarawa, a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a baya-bayan nan.

Continue Reading

Trending