Connect with us

Manyan Labarai

Gundura da ake zargi da sarewa Ɗan Bijilante hannu da fasa motar ƴan sanda ya shiga hannu

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wani Matashi mai suna Inuwa Zakari ɗan shekara 24, wanda akafi sani da Gundura, wanda ake zargi da sarewa wani Ɗan Bijilante hannu, da kuma fasa motar Ƴan Sanda, da wasu Laifuka

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM a daren Litinin, Kiyawa ya ce Matashi Gundura sun daɗe suna neman sa ruwa a jallo bisa zargin sa da tarin Laifuka.

“Gundura ya kasance abokin fitaccen ɗan Dabar nan Abba Burakita ɗa unguwar Ɗorayi da ya rasu a baya, kuma har kotu ma muka gurfanar da shi daga baya ya fita amma bai dai na abinda ya ke yi ba, a ranar zaɓen ƙananan hukumomin Kano, da ya shigo yana yunƙurin tayar da hankalin al’umma jami’an mu suka kama shi, “in ji SP Kiyawa”.

Har ila yau, Abdullahi ya ce an kama Gundura da wukake guda biyu a wani waje na matattarar Yan Daba da suke kira “Jungle” a Unguwar Dorayi.

Rundunar ƴan sandan ta ce ta kuma cafke ƙarin wasu matasa 14, da ake zargin su da aikata maban-banta laifuka, inda aka kama su a tsakanin 25 ga zuwa 27 na watan Oktoban 2024.

SP Kiyawa ya ƙara da cewa yanzu haka waɗanda ake zargin ana ci gaba da bincike a kan su a babban sashin binciken manyan laifuka na CID, da ke hedikwatar rundunar da ke Bompai a Kano, kuma da zarar an kammala za’a gurfanar da su a gaban kotu.

Manyan Labarai

Babu ɗaga Ƙafa tsakanin mu da Ƴan Daba da masu ƙwacen Waya a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Wayoyin jama’a da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye ta Anty Snaching Phone, ta gargaɗi matasan da suke addabar al’umma da faɗan Daba a cikin birnin jihar Kano, da su ƙauracewa hakan domin ba za su saurarawa dukkanin wanda ya faɗa komar su ba.

Kwamandan rundunar tsaron a jihar Kano Inuwa Salisu Sharaɗa, shi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, ya ce duk wanda suka kama da laifi musamman ma na faɗan Daba, ko ƙwacen waya ko kuma sha da dillancin kayan maye, za a ɗauki tsattsauran mataki akan sa.

 

“Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu ƙwacen Wayoyin jama’a, da Faɗan Daba, da kuma masu Sha da dallancin kayan Maye a jihar Kano, kuma duk wanda mu ka kama sai mun miƙa shi gurin da ya dace don ɗaukar Mataki, “in ji Inuwa Sharaɗa”.

 

Ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara sanya idanu wajen kula akan shige da ficen ƴaƴan su, ta yadda za su zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za’a hukunta duk ma’aikacin Shari’ar da aka samu da laifi – Babbar Jojin Kano

Published

on

Babbar jojin Kano mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta jaddada cewar kwamitin ladabtarwa na hukumar Shari’a a jihar, zai hukunta duk wani ma’aikaci a tsagin Shari’a matuƙar aka same shi da laifin cin-hanci da rashawa.

Mai Shari’a Dije Aboki ta bayyana hakan ne a yayin taron ƙarawa juna sani wanda hukumar shari’ar ta gudanar ranar Talata, a ɗakin taro na Murtala Muhammad Library da ke Kano.

Taron an shirya shi ne don tunasar da sabbin ma’aikatan Shari’a, akan nauyin da ya hau kan su don mayar da hankali sosai akan batun gujewa cin-hanci da rashawa.

Babbar mai Shari’ar Dije Abdu Aboki, ta bayyana cewar akwai takaddu masu ɗauke da lambobin wayarta da aka liƙe a bangon kotuna, kuma duk wanda aka yi wa ba dai-dai ba zai iya sanar da ita ta kan lambobin kuma za a dauki mataki akan duk ma’aikacin da aka samu da laifi.

Wakilin tashar Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, a yayin taron taron ma’aikatan Shari’a da al’umma da dama ne suka samu damar halarta.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Trending