Labarai
Maulidin Inyass: Har yanzu babu wata matsalar tsaro da aka fuskanta a Kano – Anty Snaching Force

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye ta Anty Snaching Force a Kano, ta ce kawo yammacin yau Asabar babu wata matsalar tsaro da aka samu a faɗin jihar, saɓanin wani rahoto da aka rinƙa yaɗawa a ranar Juma’a, cewar za’a iya fuskantar hakan.
Kwamandan rundunar, kuma mashawarci na musamman ga gwamnan Kano akan tsaro Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a yammacin yau Asabar 25-01-2025.
Wannan dai na zuwa ne a wani ɓangare na Maulidin Shehu Ibrahim Inyass da aka gudanar karo na 39, ranar Asabar a filin wasa na Sani Abacha Stadium da ke jihar Kano, wanda al’umma da dama daga sassan jahohihin Najeriya, da ma wasu ƙasashe suka halarta.
“Tun kafin a fara gudanar da maulidin Shehu Ibrahim Inyass, da lokacin gudanarwa har zuwa kammalawa, jami’an mu suka rinƙa zirga-zirga a cikin ƙwaryar birnin Kano, amma har zuwa yammacin yau ɗin nan ba mu samu wata matsala ta tsaro ba, “in ji Inuwa”.
A cewar sa, a zagayen da suka fara tun daga cikin daren jiya a ƙoƙarin su na daƙile matsalar tsaro yayin maulidin, sun kwana muna zirga-zirga a birnin Kano, tare da ziyartar irin su unguwannin Zango, da Hasiya Bayero, da Ƙofar Mata, da kuma gidan Murtala, da dai sauransu yankuna, baya ga zuba jami’an mu da muka yi a filin wasan na Sani Abacha Stadium.
Kwamandan rundunar tsaron ta Anty Snaching Force Inuwa Salisu, ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da basu haɗin kai domin ganin an ƙara magance matsalolin tsaro a faɗin jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.
Daga cikin manyan baƙin da suka samu damar halartar taron Maulidin akwai Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, da mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, da Malamai, da ƴan Siyasa, da sauran al’umma.

Labarai
Zan haɗa kai da hukumomin tsaro da Baturan ƴan Sanda don magance matsalolin tsaro a Kano – CP Bakori

Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Dr. Ibrahim Adamu Bakori, ya ce zai haɗa kai da dukkannin hukumomin tsaro da baturan ƴan sandan da ke kan iyakokin jihar, don ganin an sami ingantacciyar tsaro a faɗin jihar.
Dr. Ibrahim Bakori ya bayyana hakan ne a zantawar sa da manema labarai ciki har da wakilin tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 19 ga watan Maris ɗin 2025.
Ya kuma ce zai amfani da fasahar sadarwa wajan gudanar da aikin sa, tare kuma da wayar da akan al’umna kasancenwar aikin tsaro na kowa ne.
A makon da ya gabata ne dai rundunar ƴan Sanda ta ƙasa ta turo CP Ibrahim Adamu Bakori, jihar Kano, wanda ya maye gurbin Salman Dogo Garba, bisa samun ƙarin girma da ya yi zuwa matakin AIG.

Labarai
Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.
A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Labarai
Babu adalci a ƙarin kuɗin Data da na kiran Waya da aka yi a Najeriya – Human Rights

Ƙungiyar wayar da kan jama’a da kare haƙƙin ɗan adam da kuma tallafawa mabuƙata a Najeriya, ta ce Abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin kuɗin Data da na kira, al’amarin da ta kira da rashin adalci ga ƴan Ƙasa.
Daraktan ƙungiyar ta Awareness for Human Rights and Charity Foundation a Najeriya Kwamared Auwal Usman Awareness, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Lahadi.
“Ƙarin kuɗin Data da na kiran waya da kamfanonin sadarwa suka yi wa al’umma a Najeriya, abin damuwa ne, saboda ƙarin ya zo ne a dai-dai lokacin da jama’a ke fama da matsin tattalin arziƙi, da hauhawar Farashi, da wahalhalun Rayuwa, “in ji Auwal Usman”.
Ya kuma ce duba da halin mummunan tasirin wannan karin na kuɗin Data da na kiran Waya, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta umarci kamfanonin sadarwar su sauƙaƙa wa al’umma saɓanin yi musu ƙarin.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin, ta Awareness for Human rights and Charity Foundation, ta kuma buƙaci a soke ƙarin kuɗin kira da na datar da aka yi, tare da kafa dokoki da za su hana ƙara farashin ba tare da tuntuɓar al’umma ba.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, tuni dai ƴan Najeriya suka fara nuna takaicin su kan ƙarin kuɗin kira da na datar da kamfanonin sadarwa suka yi musu, lamarin da suke ci gaba da kira ga mahukunta da a rage kudaɗen bisa yadda ƙarin ya yi yawa.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su