Connect with us

Manyan Labarai

MUN BAKU WA’ADIN KWANAKI 14 KU TASHI DAGA GIDAJEN GWAMNATI

Published

on

Takaddama na kara tsamari tsakanin mazauna rukunin gidajen dake Sheikh Jaafar Mahmud Adam(Bandirawo), dana Sheik Nasiru Kabara(Amana City) wanda mallakin hukumar fansho ne ta jihar kano

Hukumar tace zata iya daukan hukuncin doka akan wadanda sukayi wa umarnin nata kunnen kashi, wajen daukar matakin hukunci domin kwato wa ‘ya’yan ta yancin rayuwar su da suka shafe tsawon lokaci suna bautawa kasar su da kuma jihar kano.

Sanarwar na fitowa ne a wannan lokaci da hukumar fansho ta jiha ke karkashin rikon kwaryar Alhaji Alasan Kibiya, koda yake sanarwar tace mabukata mallakar gidajen ko shiga haya na iya zuwa hukumar kai tsaye, a cewar kakakin ta Umar Abdu Kurmawa.

Sai dai wannan sanarwa bata shafi rukunin gidaje na kwankwasiyya ko kuma na hukumar gidaje ta jihar kano ba. Idan dai zaa iya tunawa tsohuwar gwamnatin jihar ce ta fasalta rukunin gidajen da a cewar ta, tayi ne da kyakkyawar niyyar yiwa yan fansho tanadi. Duk da ba safai ake ganin dorewar karba karbar aiki daga tsohuwar gwamnati zuwa sabuwa a Najeriya ba, amma dai za’a iya cewa sabuwar gwamnatin jihar ta mutunta wancan alkawari.

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisa ta amince da dokar gwajin cutar Ƙanjamau da ta Sikila kafin aure a Kano

Published

on

Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Har ila yau, dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Trending