Connect with us

Labarai

Shirin wanzar da zaman lafiya a Zamfara ya karbi mutane 372 da makamai

Published

on

Shirin wanzar da zaman lafiya a Zamfara ya karbi mutane 372 da makamai

Tubabbun ‘yan bindiga a jihar zamfara sun mika mutanen da suka yi garkuwa da su mutum 372 tare da bindigogi 240 ga shirin wanzar da zaman lafiya na jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara Usman Nagogo, wanda shi ne shugaban kwamitin na wanzar da zaman lafiya, ya bayyana hakan a jiya Lahadi 22 ga watan Satumba yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na kwamitin a garin Bakura.

Haka kuma ya kara da cewa sun gano ‘yan ta’addar ba wai iya Fulani makiyaya ba ne kamar yadda ake ta fada a baya, yana mai cewa, ‘yan ta’addar sun fito ne daga kabilun kasar nan daban-daban.

Kwmishinan ‘yan sandan na jihar zamfara ya kuma zargi jami’an tsaro na sa kai da ake kira da ‘yan sintiri da kara tazzara ayyukan ta’addanci a jihar.

Usman Nagogo ya kuma bayyana gamsuwarsa da irin nasarar da kwamitin ya samar daga kafa shi zuwa yanzu, yana mai cewa a baya an rufe wasu daga cikin kasuwannin jihar sakamakon matsalar tsaro, amma a yanzu an bude kasuwar kuma Fulani na gudanar da harkokin kasuwancin sub a tare da wata matsala ba.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma bukaci al’ummar jihar das u mara wa kwamitin baya tare da taya su da addu’o’in samun nasara a ayyukan su.

Ya kuma kara da cewa yayin taron an tattara masu ruwa da tsaki a rikice-rikicen jihar da suka hadar da ‘yan sintiri da shugabannin Fulani masu rike da sarautun gargajiya da sauransu.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending