Connect with us

Hangen Dala

Saurari shirin Hangen Dala na ranar Juma’a 27 09 2019

Published

on

HANGEN DALA 09 10 2019Za muyi amfani da kudin VAT wajen bunkasa Ilimi.

A cikin shirin Hangen Dala na ranar Juma’a 27 09 2019 kunji cewa kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ta musanta rade-radin da ake na cewa akwai jikakkiya tsakanin ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ofishin mataimakinsa farfesa Yemi Osinbajo.

Sannan kunji cewa kotun kolin Najeriya dake Abuja ta kori daukaka karar da gwamnan Kano Dr. Abullahi Umar Ganduje  da jam’iyyar APC suka yi na kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara, wadda ta ayyana cewar babu laifi ga jam’iyyar PDP da dan takarar ta su karo shedu a gaban kotun sauraron kararrakin zabe.

Download Now

Ayi Sauraro Lafiya.

 

Hangen Dala

Gaya Ajingi Albasu:- Dan majalisa ya raba kayan abinci

Published

on

Dan majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu Dakta Ghali Mustafa Fanda ya fara rabon tallafin kayan abinci ga al’ummar kananan hukumomin uku.

 

Yayin rabon tallafin kayan abincin, Dakta Ghali Mustafa yace yayi rabon tallafin ne domin fara sauke nauyin al’ummar da yake wakilta.

 

” Wannan tallafi zamu bayar da shi ne domin fara sauke nauyin al’ummar da suka zabe mu, kuma wannan shi ne karon farko, kuma yayi daidai da bukatar al’umma a yanzu, shiyasa muka fara da tallafin kayan abinci”.

 

“A cikin wannan tallafi mutane kimanin dubu ashirin ne zasu amfana, wanda zamu bayar da buhunan Shinkafa da Gero da Garin masara.”

 

Haka kuma ɗan majalisar ya bayar da tallafin Naira miliyan ashirin ga matasan kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu.

 

Sai kuma ɓangaren dalibai mata, wanda shima a yau dan majalisar ya dauki nauyin karatun dalibai mata guda 60 a bangaren lafiya.

 

Haka kuma cikin jawabin nasa Hon Ghali ya kuma ce nan gaba kadan zai bayar da tallafin taki ga manoma, da kuma farfaɗo da dukkanin rijiyon burtsatse na kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu a wani mataki na samar da ruwan sha.

 

Da yake nasa jawabin mataimakin gwamnan Kano Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo wanda ya samu wakilcin mai baiwa Gwamna Shawara kan harkokin siyasa Hon Sunusi Surajo Kwankwaso kira yayi ga sauran wakilan al’umma da suyi koyi da Dakta Ghali Mustafa Fanda wajen ayyukan alkhairi da kuma jin kan al’umma.

 

Haka kuma Hon Sunusi Surajo ya yabawa dan majalisar bisa bayar da tallafin ga ƙananan hukumomin uku.

 

Taron dai wanda ya gudana a cikin Islamic Centre na karamar hukumar Gaya ya samu halartar manya, da kuma jagororin yankunan uku, kuma nan take Dan majalisar Tarayya Dakta Ghali Mustafa ya fara rabon tallafin

Continue Reading

Hangen Dala

Shugaban kasa ya bayar da umarnin bude Boda

Published

on

Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin kasar nan.

Cikin sanarwar da ya fitar shugaban ya ce duk wata iyaka dake tsakanin Nigeria da jamhuriyar Nijar a gaggauta bude ta.

Karin bayani na nan tafe…

Continue Reading

Addini

Yanzu yanzu:- Daurawa ya koma mukamin sa

Published

on

Bayan wata ganawa da akayi tsakanin gwamnan Kano da kuma zauren hadin kan malaman jihar karshe an cimma matsayar sheik Aminu Ibrahim Daurawa zai koma kujerar sa ta shugabancin hukumar Hisba.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa yace bayan dogon nazari kungiyar ta fahimci shedan ne ya so shiga tsakanin gwamnan Kano da sheik Malam Aminu Daurawa.

A baya bayan nan ne dai gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf yayi wasu kalamai dake nuna rashin gamsuwa da ayyukan hukumar Hisba wanda kalaman ya sabbaba saukar Malam Daurawa daga mukamin sa.

A daren wannan Litinin dai zauren hadin kan malaman suka yi wannan zama da gwamnan Kano, inda a karshe aka cimma matsayar sulhu kuma nan take Malam Aminu Daurawa ya amince zai cigaba da jagorantar hukumar ta Hisba.

Continue Reading

Trending