Connect with us

Manyan Labarai

Diyyar miliyan 50 nake nema daga Hadiza Gabon -Amal.

Published

on

Babbar kotun tarayya dake zaman ta a unguwar gyadi-gyadi ta cigaba da sauraron karar da fitacciyar yar wasa Hausa Amina Amal ta shigar, domin neman hakkin cin zarafi da yar was an tace Hadiza Gabon tayi mata.

A watannin baya ne dai Amal ta garzaya gaban kotun mai lamba biyu domin neman hakkin cin zarafin da tace anyi mata a matsayin ta na bil’adama, matakin da lawyoyin wadda ake karar wato Hadiza Gabon suka yi kakkausan suka akai cewar kotun ba ta da hurumin sauraron karar, tunda abinda mai kara ke neman hakki akai ya faru ne a jihar kaduna.

Sai dai kuma mai shari’a O.A Egwuata ya fara sauraron karar a yau Alhamis, inda aka saurari bayanai daga bangarorin biyu, wanda ya hadar da karbar takardu bukatu da kuma bayar da ba’asi akan abinda ya wanzu a tsakani.

Bayan kammala karbar bayanan ne mai shari’a Egwuata ya dage zaman kotun akan wannan al’amari har sai ranar Laraba 23 ga watan Oktobar nan, domin hukunci akai.

Idan dai za’a iya tunawa a kwanakin baya ne wani faifan bidiyo ya zagaya a kafafen sada zumunta, mai dauke da sa-insa a tsakanin taurarin biyu.

Labarai

Rahoto: hukumar NDLEA na hukunta duk jami’in ta da ya yi laifi – Dakta Ibrahim Abdul

Published

on

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kasa reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul ya ce, duk lokacin da ya samu daya daga cikin ma’aikatan su ya yi laifi, ya na hanzarin daukar matakin kora ko kuma hukuncin da ya dace.

Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, lokacin da yake mayar da martani a kan matasan da a ke zargin sun fada ruwan kududdufi lokacin da hukumar ta NDLEA ta kai simame yankin Dan Agundi da ke jihar Kano.

 

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa 2 sun gurfana a kotu kan zargin raunata jami’an KAROTA 3

Published

on

Kotu mai lamba 47, da ke rukunin kotunan majistret a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Huda Haruna Abdu, wasu matasa biyu Yunusa Sunusi da kuma Muhammad Babagana, sun gurfana a kotun da tuhumar a kan yi wa wasu jami’an hukumar KAROTA rotse, da suka hada da Usamatu Abdullahi da Sulaiman Musa da kuma Abdulkadir Isma’il.

Ana tuhumar matasan da laifuka guda uku, laifin hada baki da cin zarafi da kuma haddasa mummunan rauni, laifukan da suka saba da sashi na 93 da sashi na 264, sai kuma 247 na kundin laifuka, bayan kuma an karanta musu kunshin tuhumar zargin da a ke yi musu duk sun musanta.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotu ta fara sauraren shari’ar matar da a ke zargi da kazafin maita

Published

on

Wata mata ta gurfana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola a kan zargin bin gari tana yada labarin cewa makwabciyarta da ‘ya’yanta duk mayu ne.

Tun da fari dai matar da a ke zargi da maitar, ta garzaya ofishin ‘yan sanda, tana karar makwabciyar tata, daga bisani kuma ‘yan sanda su ka tattara bayanai su ka mika su kotu domin fara sauraran shari’ar, bayan kuma karantawa matar mai yada labarin maita kunshin tuhumar ta musanta, inda kotu ta dage sauraren shari’ar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!