Connect with us

Rahotonni

Me kuka sani game da shari’ar musulunci a Najeriya?

Published

on

Malamai da mabiya addinin musulunci a jihohin Arewacin kasar nan sun dauki tsawon lokaci suna fafutukar ganin an kafa shari’ar musulunci a sassa daban-daban na kasar.

Biyo bayan kiraye-kiraye na mabiya addinin musulunci ya sanya gwamnan jihar Zamfara a wancan lokacin Ahmad Sani Yariman Bakura ya sanar da cewa jihar Zamfara zata fara aiki da tsari irin na shari’ar addinin musulunci a ranar 27 ga watan Octoba na shekarar 1999.

Jihar Zamfara itace jiha ta farko da ta fara kaddamar da shari’ar musuluncin a ranar 27 ga watan Janairu na shekara ta 2000, sai jihar Kano dake biye mata baya inda gwamnan jihar na wancan lokaci Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da shari’ar a watan 6 na shekara ta 2000.

Jihar Sokoto da kuma jihar Katsina sun biyewa jihar Kano baya inda suma suka kaddamar da tsarin shari’ar musulunci a karshen shekarar ta 2000.

Jihohin Bauchi, Borno, Jigawa, Kebbi da kuma jihar Yobe suma sun bi sahun sauran jihohin da suka kaddamar da shari’ar tun da farko a shekarar 2001.

Su kuwa jihohin Kaduna, Niger da kuma jihar Gombe sun kaddamar da shari’ar musulunci ne a wasu sassa na jihohinsu da musulmai ke da rinjaye, kasancewar suna da al’umma da dama masu mabam-bamta addini a jihar.

Al’ummar musulmi dai sunyi farin ciki matuka da kaddamar da shari’ar a wancan lokaci.

RUBUTU MASU ALAKA:

An sauke masu rike da mukamai a Hisbah

Munyi hannun riga da rashawa- Hisba

Hisbah ta bukaci maza da su dinga barin kananan ‘ya’yansu a wajen iyaye mata idan an samu rabuwar aure

Continue Reading

Rahotonni

Al’umma na cigaba da raya daren Mauludi a Kano

Published

on

Al’ummar musulmi daga ko ina a fadin duniya na cigaba da gabatar da bukukuwan maludi domin murnar zagayowar ranar da aka haifi fiyayyen halitta manzon tsira Annabi (s.a.w), wanda ake yi duk shekara a wannan wata na Rabi’ul Auwal da muke ciki.

Haka abin yake a nan jihar Kano, inda tun kafin shigowar watan al’umma kama daga yara da manya, maza da mata ke ta shirya tarukan mauludi ba dare ba rana a sassa daban-daban na jihar Kano.

Ana kawata wurin Mauludi da kayan ado

Musulmi kan kawata wuraren taron Mauludi da ado kala-kala masu daukar hankali domin girmamawa ga Manzon Allah (s.a.w).

Me ake yi a taron Mauludi?

Musulmai na amfani da taron Mauludi wajen karantar da tarihin manzon tsira Annabi (s.a.w) da kuma koyar da ibadu bisa tsari da tarbiyyar addinin Musulunci.

Haka kuma akan rera kasidun bege, sannan akan baiwa dalibai karatuttuka wanda suke haddacewa su karanto a ranar Mauludi.

Al’umma na yin ankon kayan sawa na musamman domin ranar bikin, haka kuma akan yi girki kala-kala duka dai domin wannan biki.

Ana yin Mauludi ba dare ba rana a Kano

Al’umma na gudanar da bikin mauludi ba dare ba rana a birnin Kano, domin kuwa duk inda ka zaga a lungu da sako na jihar Kano zaka iske al’umma a sassa daban-daban na gudanar da bukuwan na Mauludi.

Gobe Lahadi shi ne dai-dai da ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal ta wannan shekarar, wato dai-dai da ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi (s.a.w), wannan rana tana da matukar muhimmanci ga musulmi.

Continue Reading

Rahotonni

‘Yan Soshiyal Midiya na neman a soke lefe

Published

on

Wani batu dake cigaba da jan zare a shafukan sada zumunta shine batun A Soke Lefe da masu amfani da shafukan ke ta kiraye-kiraye a kai, wanda ake ta tafka muhawara tsakanin samari da ‘yan mata.

Sai dai ‘yan mata na ta sukar wannan bukata, inda su ma suke ganin matukar za’a soke lefe to sai an hada da kayan daki.

Wannan dai ba sabon abu bane a wurin masu amfani da soshiyal midiya, domin kuwa sun saba tsokano sama da kara amma a iya shafukan, kafin mu waiwayo muku wasu daga batutuwan da ‘yan soshiyal midiya suka sha tafkawa, ku kalli yadda suke tafka cecekuce a yanzu kan kokarin su na ganin an soke lefe a kasa.

Waiwaye:

A shekara ta 2016 cecekuce da masu amfani da soshiyal midiya suka yi, ya tilastawa gwamnatin tarayya dakatar da shirinta na gina cibiyar shirya fina-finai a Kano wato Film Village.

Haka ma dai a shekarar 2018 da ta gabata, ‘yan soshiyal midiya sun bada gudummuwa matuka wajen ganin an ceto wata matashiya ‘yar jihar Kano mai suna Zainab Habib Aliyu wadda mahukunta suka tsare a kasar Saudia bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

Labarin matashin nan Yunusa Yellow shi ma batu ne da ya nuna tasirin ‘yan soshiyal midiya a Arewacin Najeriya wanda yanzu haka mahukunta sun shiga cikin lamarin nan.

Na baya-bayan nan shi ne batun yaran Kano 10 da aka sace zuwa kudancin kasar nan inda ‘yan soshiyal midiya suka kirkiri wani Hashtag mai suna #Kano9 wanda yayi karfi sosai a shafin Twitter da Facebook da sauran shafukan intanet.

Irin wannan dai sun sha faruwa birjik, dukda cewa manazarta na ganin akwai tarin batutuwa marasa muhimmanci da masu amfani da soshiyal midiya keyi kamar labarin shugaba Buhari zai kara aure, ko na Aisha Buhari tayi yaji da makamantan su.

Abin jira dai a gani shi ne ko wane tasiri wannan yunkuri na Asoke Lefe zaiyi?

Rubutu masu alaka:

Kannywood: Kotu ta kori shari’ar Amina Amal

Jamila Nagudu ce ta can-canta da zama gwarzuwar Kannywood –Kamaye

Continue Reading

Trending

en_USEnglish
en_USEnglish