Connect with us

Shari'a a Aikace

Masu hannu da shuni su dinga taimakawa na kasa dasu – Dan Baito

Published

on

Wani lauya mai zaman kansa a jihar kano Barista Umar Usman Danbaito, ya bukaci mahukunta da su ringa sassautawa na kasa dasu domin samun rayuwa mai inganci.

Barista Danbaito ya bukaci hakan ne ta cikin shirin shari’a a Aikace da ya gudana a gidan radiyon Dala, inda yace doka ce ta tanadar da cewa mahukunta su samar da Abubuwan more rayuwa ga wandanda suke bukata a kowanne bangare.

Ya kuma ce suma al’umma musammamm mawadata na da rawar takawa wajen taimakawa wadanda suke kusa dasu.

Ya kara da cewa su ma malaman boko da na islamiyyu su na da gudunmawar da za su bayar ga yaran da ake kai musu don su basu ilimi ingantacce.

Haka zalika Barista Danbaito, ya ce duk al’ummar da aka baiwa Amana a hannun  Abun tambaya ne ranar gobe kiyama.

Addini

Yanzu yanzu:- Daurawa ya koma mukamin sa

Published

on

Bayan wata ganawa da akayi tsakanin gwamnan Kano da kuma zauren hadin kan malaman jihar karshe an cimma matsayar sheik Aminu Ibrahim Daurawa zai koma kujerar sa ta shugabancin hukumar Hisba.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa yace bayan dogon nazari kungiyar ta fahimci shedan ne ya so shiga tsakanin gwamnan Kano da sheik Malam Aminu Daurawa.

A baya bayan nan ne dai gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf yayi wasu kalamai dake nuna rashin gamsuwa da ayyukan hukumar Hisba wanda kalaman ya sabbaba saukar Malam Daurawa daga mukamin sa.

A daren wannan Litinin dai zauren hadin kan malaman suka yi wannan zama da gwamnan Kano, inda a karshe aka cimma matsayar sulhu kuma nan take Malam Aminu Daurawa ya amince zai cigaba da jagorantar hukumar ta Hisba.

Continue Reading

Labarai

Kotu ta yankewa sojan da ya kashe shek Bagoni hukuncin kisa

Published

on

Wata babbar kotun Jihar Yobe da ke garin Pataskum ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan jami’in sojan nan Lance Corporal John Gabriel da ya kashe fitaccen malamin addinin Musuluncin jihar, Sheikh Bagoni Aisami.

Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ga abokin aikin sojan mai suna Lance corporal Adamu Gideon da ya taimaka wajen aikata kisan.

A hukuncin da ya zartar a ranar Talata, Alkalin kotun, mai shari’a Usman Zanna Mohammed, ya ce kotu ta samu John Gabriel da laifin kisan kai, shi kuma Adamu Gideon da laifin taimakawa wajen hadin bakin aikata laifin.

 

Alkalin kotun ya ce mutanen biyu sun kasa tabbatar wa kotun cewa ba su da laifi, don haka aka yanke musu hukunci daidai da laifinsu.

 

Idan za a iya tunawa a watan Agustan 2022 ne aka kama jami’in sojan bisa zargin yi wa sheikh Goni Aisami kisan gilla a wani wuri da ke yankin Karamar Hukumar Karasuwa a Jihar Yobe, kusa da garin Gashua bayan da malamin ya ragewa sojan hanya a motarsa daga garin Nguru.

Continue Reading

Labarai

Ku guji kawo tsaiko a shari’a – Alkali Waiya

Published

on

Alkalin babbar kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a Kasuwar Kurmi Shahuci Barista Abdu Abdullahi Waiya, ya shawarci lauyoyi da su gujewa kawo tsaiko a shari’ar bisa rashin mahimmancin da hakan ke da shi.

 

Barista Abdu Abdullahi Waiya ya bayyana hakan ne jim kaɗan da karɓar shaidar zama lauya a birnin tarayya Abuja, yana mai cewa kawo tsaiko ga shari’u yakan haifar da babbar matsala, a dan haka bai kamata lauyoyi da ɓangarorin Shari’a su rinƙa jan Shari’a da za tayi tsayi har ta kai ga an samu tsaiko ba.

 

Ya kuma ce ko musulunci ma yayi hani da kawo tsaiko a cikin kowanne al’amari, a dan haka ya buƙaci al’umma da su kasance masu sanya gaskiya a dukkanin lamurransu.

 

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito Barista, kuma Alƙali Abdu Waiya ya kuma bayyana farin cikinsa bisa samun matsayin zama lauya, wanda ya karɓi shaidar zama lauyan a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Continue Reading

Trending