Baba Suda
Wata matashiya ta sha fiya-fiya akan saurayi
Wata matashiya mai suna Hauwa da ake zargin ta sha maganin kwari da nufin hallaka kanta saboda tsananin soyayya.
Mahaifiyarta ce tayi barazanar raba su saboda tayi zargin cewar saurayin kamar yana yaudarar ta.
Matashiyar mazauniyar unguwar fanshekara ce a karamar hukumar Kumbotso dake nan Kano ta fara soyayya da wani mai sana’ar cajin waya da kuma sayar da maganin kwari, kasancewar Hauwa na zuwa shagun sa don yin zance.
Sai dai mahaifiyar budurwar ba ta son tarayyar su, ko miskala-zarra bayan da ta nemi Hauwa ta rabo da shi, yayin da ita kuma taki amincewa da matakin mahaifiyarta.
Don haka ne mahaifiyar ta je wajen saurayin ta kuma yi masa kashedin ya rabu da ‘yarta.
Hakan ne ya fusata matashiyar ta yi yunkurin sha fiya-fiya a shagun saurayin nata.
Tuni dai aka garzaya da Hauwa Asibiti don ceto rayuwarta, kamar yadda wani shaidar gani da ido ya shedawa wakilin Dala Fm Tijjani Adamu.
Baba Suda
Matashi ya shiga hannu bisa zargin sa da yin baɗala da Akuya
Jami’an tsaron jihar Ogun na Amotekun, ta kama wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila, bisa zargin laifin yin lalata da wata Akuya.
An kama Ismaila mai shekaru 18 a garin Ilu-Tuntun Olorunsogo, Ajowa, cikin karamar hukumar Ifo ta jihar.
Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce, kama matashin ya biyo bayan karar da wani Jimoh Opeyemi ne ya yi, wanda ya ga Ismaila a lokacin da yake yin lalata da Akuyar.
Jimoh Opeyemi, ya je wajen wani gini sai ya hangi wanda ake zargin ya na amfani Akuyar.
Akinremi ya ce, Opeyemi ya ƙwarma ihu, inda ya jawo hankalin jama’a a yankin ciki har da wani jami’in Amotekun Corps, wanda ya samu nasarar cafke wanda ake zargin.
Baba Suda
Toro: Namijin Agwagwa ya shafe tsawon shekaru 13 a raye – Umaru Tunkuli
Wani matashi mai suna Umaru Yahaya mazaunin layin Kuka Sani Mai Nage (A), a jihar Kano, ya tabbatar mana da cewa Namijin Agwagwar (Toro) da ya ke kiwao ya shafe tsawon shekaru 13 ya na raye a wajen shi ba tare da ya gudu ba.
Matashin Umaru Tunkuli, ya ce a yanzu haka bay a sha’awar ya yanka wannan Toro, hasali ma ya kai shekaru 20 ya na kiwon Agwagi.
Ga tattaunawar su da wakilin mu Tijjani Alfindiki.
Baba Suda
Rahoto: Zan bayar da kudin fansa domin a dawo da Kyanwa ta – Matashi
Wani matashi a yankin unguwar Farawa dake karamar hukumar Kumbotso, Kawu Rufa’I, ya ce a kan Magen da ya ke zargin an yi masa garkuwa da an raba shi da abar kaunar shi, sakamakon yadda suka shaku da juna.
Kawu Rufa’I yacce zai dauki matakin shari’a mudum ya yi artabu da mutum da ya yi garkuwa da Magen, wanda ya bayyana cewa tun a baya sai da a ka dauke ta duk da furucin da a ka yi masa cewa za a dauke ta.
Wakilin mu Tijjani Adamu wanda ya tattauna da matashin ya aiko mana rahoto.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su