Connect with us

Labarai

An gano ‘yan makarantar marin da aka boye a Daji

Published

on

Hukumomi a nan Kano sun gano wasu wasu matasa da ake tsare dasu a wata makarantar gyaran tarbiyya wato ‘Yan mari mai suna Daiba dake unguwar Rijiyar Lemo a nan Kano.

A yayin wani sumame da kwamitin gaggawa da gwamnatin jihar Kano ta kafa wanda zai tsaftace makarantun marin ya kai makarantar ta Daiba ya samu nasarar tseratar da wasu daliban makarantar da aka boyesu a wani daji.

Wakilin mu Abba Isa Muhammad ya zanta da wasu daliban inda suka bayyana masa cewa bayan da aka samu labarin cewa gwamnati ta kafa kwamitin da zai tsaftace makarantun mari shine ya sanya mahukuntan makarantar suka kwashe su daga nan suka sauya musu wuri.

Shima a nasa bangaren shugaban makarantar Malam Tijjani Sharif Sale ya bayyana cewa jami’ai sun zo makarantar sun kuma duba tsarin da suke gabatar da gyaran tarbiyya ne, sannan a shirye suke su baiwa kwamitin goyon baya domin gudanar da ayyukansa.

Har ila yau wakilin mu Abba Isa Muhammad ya tattauna da shugaban kwamitin da gwamnatin jihar Kanon ta kafa Mallam Muhammad Tahar Baba Impossible, wanda ya bayyana cewar akwai kyakkyawar manufa da ta sanya gwamnatin take son tsaftace makarantun yammarin.

RUBUTUKA MASU NASABA:

Bana sakawa dalibai na mari –Mallam Mamman mai ‘yan mari

Matasa a guji shaye-shayen kwayoyi -Danmari

Labarai

An kama wani matashi da zargin sacewa almajirai kayan sawa

Published

on

Shugaban kungiyar Bijilante na yankin unguwar Hausawa dake karamar hukumar Tarauni a Kano, Usaini Haruna Kailo, ya shawarci iyaye da su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su domin rayuwar su ta zama abar koyi a nan duniya dama ranar gobe kiyama.

Usaini Kailo ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, bayan kama wani matashi da su ka yi, da zargin diban kayayyakin sawa na almajirai cikin wata makarantar tsangaya a unguwar Hausawa ‘yan babura.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyar ya’yan su babu shakka za a rage yawaitar samun lalacewar su”.

Da yake nasa jawabin matashin da a ka kama ya ce” Wannan shi ne na farko kuma shi ne na karshe ba zan kara satar kayayyakin mutane ba”.

Wakilin na mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewa, Kwamandan Bijilanten Usaini Haruna Kailo ya ce, za su mika matashin da su ka kama wajen jami’an tsaro domin matakin da ya dace a kan sa domin hakan ya zama izina ga sauran matasa.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish