Connect with us

Labarai

Jarumi Madagwal na fama da rashin lafiya

Published

on

Fitaccen jarumin barkwancin nan Ali Artwork wanda aka fi sani da Madagwal ya aike da sakon godiyarsa ga daukacin masoyansa da suka taya shi da addu’o’I sakamakon rashin lafiya da yayi.

Madagwal ya wallafa sakon godiya ga dimmin masoyansa ta shafin sa na Instagram, sannan yayi godiya ga Allah mahalicci.

“Ina Kara Godiya Gareku Masoyana da Abokaina da ‘Yan Uwana da Iyayena da iyayen Gidana da duk wanda ya ta yani da addu’ar samun Lafiya da wanda na sani da wanda ma ban sani ba nagode nagode nagode sosai Allah ya bar zumunci”

Kafin jarumin ya wallafa wannan bayani dai, an ta yada wasu hotunansa a gadon asibiti a kafafan sada zumunta.

Masoya jarumin da dama ne dai suka rika yi masa fatan alkhairi da addu’ar samun lafiya.

Labarai

Kano: Matasa su nemi ilimi maimakon wasanni-Sardaunan Gama

Published

on

Sardaunan Gama, Babba Lawan, ya gargadi matasa da su tashi tsaye wajen neman ilimin addini da na zamani maimakon mayar da kai a harkokin wasanni da kuma kallon kwallon kafa.

Sardaunan na Gama, Babba Lawan, ya bayyana hakan ne a wajan saukar karatun alkur’ani mai girma na daliban makarantar Ibn Abbas, dake Unguwar Gama a karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Ya ce” Matasa su mayar da hankalin su wajan neman ilimi rayuwar su domin inganta ta, maimakon a yanzu za ka ga matashi ya dukufa a harkokin wasanni, yafi a ce su nemi ilimin zamani da na alkur’ani”.

A nasa bangaren shugaban makarantar, Malam Abubakar Idris Gama, ya ce” Akwai bukatar karin hadin kai daga iyayen dalibai, musamman wajan biyan kudin makaranta da ake karba duk karshen wata domin gudanar da harkokin makaranta”.

Wakilin mu Abubakar Sabo, ya rawaito cewa, dalibai talatin da bakwai ne suka sauke wandanda suka hadar da Maza da Mata.

 

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano ta bukaci matasa su nemi ilimin aure kafin yin sa

Published

on

Daraktar kula da al’amuran mata a ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Kano, Hajiya Kubura Ibrahim Dan Kani, ta yi kira ga mata da maza masu shirin yin aure dasu kasance masu ilimin aure kafin yin sa.

Hajiya Kubra, ta bayyana hakan a zantawar ta da gidan rediyon Dala yau Talata.

Ta ce” Maza da mata su nemi ilimin zamantakewar aure kafin su yi aure sakamakon sabani da ake samu domin wasu ma’auratan ba su san me ne auren ba, kawai suna yi ne auran kai tsaye ba tare da sun san muhimmancin sa ba. Kuma mun shirya tsaf a yanzu domin wayar da kan wasu daga cikin maza da mata masu shirin yin aure domin basu bita ta musamman a kan auratayya”. A cewar Kubura.

Sannan kuma hukumar mu tan a tallafawa marayu da marasa galihu a birni da karkara ta hanyar koya masu sana’o’in dogaro da kai, kuma duk wani mai bukatar hakan kofar mu a bude ta ke wajen tallafa masa”. Inji Kubura.

Wakilin mu Nasir Kalid Abubakar,ya rawaito cewa daraktar hukumar a shirye suke da su bada tallafi ga masu bukatar hakan, musamman a bangaren koya mu su sana’o’in dogaro da kai tare da zamantakewar aure.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

An tono wata gawa da aka bunne a Kano

Published

on

Tun da fari dai Babbar kotun shari’ar Muslunci ce mai zaman ta a  kofar Kudu ce karkashin mai shari’a Ustazu Ibrahim Sarki Yola, ta yi umarnin a yiwa gawar sutura kasancewar hukumar Hizba ta roki kutun ta yiwa asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano Umarnin su bayar da gawar wani mai suna, Abdullahi Obinwa, inda a nan ne aka samu akasi aka musanya gawar da ta wani dan kabilar Ibo mai suna Basil Ejensi, bayan kuma ya cika umarnin kotun da kwanaki bakwai da binne shi.

Sai dai wasu ‘yan kabilar Ibo suka garzaya kotun ta mai shari’a Ustazu Ibrahim Sarki Yola, suka yi roko a gaban kotun cewar anyi musu musayar gawa domin haka kotun ta yi umarni a kwakulo gawar da ta bayar da damar binewa kwani bakwai da suka gabata domin dai tasu ce bata wadanda suka nema ba tun da fari.

Bayan jin kowanne bangare mai shari’a Ustazu Ibrahim Sarki Yola, ya bayar da wani umarnin cewar a samu rakiyar jami’an tsaro zuwa makabartar domin tono gawar mai kwanaki bakwai a bunne ta a waccan makabartar ta unguwar Gandun Albasa dake Karamar Hukumar Birnin Kano, da yammacin ranar Litinin dinnan,

Harma bayan kwakulo gawar daga kabarinta ankuma damkata ga Lauyan gawar Masalinas Duru, harma lauyan ke cewa” Hukuncin kotun ya yi mana dadi sakamakon an bamu gawar mu”.

Shima limamin da ya sallaci gawar Malam Aminu Ahmad Adam, ya ce” Kuskure ne an riga an yi shi kuma babu wanda ya wuce ya aikata shi”.

Sai dai Jami’in hukumar Hizba mai lura da Makabarta, Malam Jamilu, wanda su ne suka yi kara ta farko ya ce” Na yi mamaki  game da wannan lamarin da ya kasance”.

Suma wasu da suka ganewa Idanuwansu yadda Ka hako gawar sunce har da jami’an tsaro a rakiyar kuma a gaban su aka kwakulo gawar sannan aka daura shi a gadon asibiti kuma tuni ‘yan uwan sa suka tafi da shi.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish