Connect with us

Labarai

Zaman lafiya ya dawo a Zamfara – SP Shehu

Published

on

Rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta bayyana cewar zuwa yanzu zaman lafiya ya samu a jihar.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar zamfara SP Shehu Muhammad ne ya bayyana wa wakilin gidan rediyon Dala Yusuf Nadabo Ismail a yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar.

SP Shehu ya bayyana cewar tun bayan zuwan kwamishinan ‘yansandan jihar CP Usman Na Gwaggo ya himmatu da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su dan neman kudin fansa.

Na Gwaggo ya kuma ce rundunar ta kubutar da mutane sama da 130 ba tare da biyan kudin fansa ba.

Haka zalika sun kama wadanda ake zargi da hannu wajen rikicin Zamfara tare da kwato bindigogi kirar AK 47 masu tarin albarusai.

SP Muhammad ya kara da cewar rundunar tana aiki kafada da kafada da kwamitin fararen hula masu hulda da ‘yansanda wato PCRC.

Har ila yau, rundunar ta yabawa gwamnan jihar Bello Matawalle bisa gudunmawar da yake baiwa bangarorin tsaro.

Labarai

Ba zamu lamunci yin duk abin da ya saɓa da tsarin Musulunci ba a Kano – Hukumar Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ba za ta lamunci yin duk abinda ya saɓa da koyarwar addinin Musulunci, ko kuma yin duk abin da ya saɓawa tarbiyya ba.

Muƙaddashiyar babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano a ɓangaren Mata Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ce ta bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala Walima tare da yin addu’o’i da yabo ga Ma’aiki S.A.W, da aka gudanar yau a harabar hukumar, gabanin fita zagayen bikin Takutaha.

Dakta Khadijah Sagir Sulaiman da ta jagoranci ƴan Hisbar zagayen bikin Takutaha ranar Lahadi 22 ga watan Satumban 2024, a Kano, ta ce fatan hukumar shi ne umarni da kyakkyawa gami da hani da mummunan aiki.

A cewar ta, “Ba zamu yadda da cewa a fito ayi baɗala ko kuma yin abinda ya saɓawa tarbiyya ba da sunan nuna soyayya ga shugaba Sallallahu alaihi Wasallama, duk wanda ya yi abinda ya saɓa doka za mu ɗauki mataki akan sa, “in ji Dr. Khadijah”.

Wakiliyar Dala FM Kano Hadiza Balanti ta rawaito cewa, yayin zagayen bikin Takutahar jami’an hukumar Hisbar sun samu nasara sanya wasu matasa da canza shigar matan da suka yi zuwa ta maza, musamman ma wasu matasa da suka yi shigar mata wajen yin kwalliyar mata da kuma sanya kayan matan, tare da aske gashin wasu matasa maza da suka yi askin da bai dace ba a kan su.

Continue Reading

Labarai

Komawa makaranta: Ya kamata Gwamnatin Kano ta wadata motocin jigilar ɗalibai – Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da ta ƙara wadata motocin ɗaukar ɗalibai a faɗin jihar, domin taimakawa ɗalibai wajen jigilar su zuwa makarantn su, domin samun dama wajen zuwa makaranta akan lokaci.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar a matakin ƙasa Tasi’u Idris Idris (Soja) ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Talata 17 ga watan Satumban 2024.

Ya ce ƙara wadata motocin daga ɓangaren gwamnatin jihar Kano, ka iya taimakawa ɗalibai wajen zuwan su makaranta akan lokaci ba tare da makara ba, musamman ma bisa la’akari da yadda wasu masu baburan adai-dai ta sahu suke ƙauracewa ɗaukar su bisa tsadar fan Fetur.

“Muna kira ga matuƙa baburan Adai-dai ta sahu da ke jihar Kano, da su rinƙa ɗaukar ɗaliban da suka fito domin zuwa makaranta, domin taimakawa karatun su, “in ji Tasi’u”.

Sai dai jami’ar da ke kula da harkokin ilmin Ƴaƴa Mata a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Amina Kasim, ta ce tun kafin a koma makaranta ma’aikatar Ilmi ta yi shiri wajen inganta motocin da za su yi jigilar ɗalibai zuwa makarantun su.

Amina Kasim ta ci gaba da cewa, “Tun da safiyar wannan rana motocin mu suka fara zirga-zirga suna ɗaukar ɗalibai ana kai su makaranta, waɗanda aka gani jibge a bakin hanya irin waɗanda suka raina motocin gwamnati ne suke cewa wai ta sada ce, “in ji ta”.

Wannan dai na zuwa ne yayin da daliban makarantun Sakandire da na Firamare suka koma makarantun su bayan dogon hutun da suka sha, domin fara karatu zangon farko na shekara ta 2024/2025.

Continue Reading

Labarai

Za’a fara yiwa ɗalibai gwajin Ƙwaya kafin su shiga kwaleji a Kano

Published

on

Kwalejin fasaha ta jihar Kano, Poly Technic, za ta fara gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ga ɗaliban da za su nemi gurbin karatu a shekara mai zuwa ta 2025.

Shugaban kwalejin Dakta Abubakar Umar Faruk, ne ya bayyana hakan yau Asabar, a yayin taron wayar da kan ɗalibai illar Shan miyagun ƙwayoyi domin kare kai daga cin zarafin Jinsi, da ƙungiyar ɗaliban kwalejin ta shirya.

Taron ya gudana ne a ɗakin taro na Farfesa Hafiz Abubakar, da ke reshen kwalejin na matan fada, da ke jihar Kano.

Shugaban kwalejin wanda maga-takardar makarantar Muhktar Ibrahim Bello, ya wakilta, ya ƙara da cewar matakin gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyin hakan zai taimaka wajen yaƙi da miyagun kwayoyi a kwalejin da ma jihar Kano.

Da yake na sa jawabin akan dabarun kaucewa Shaye-shaye kwamandan hukumar NDLEA ta ƙasa reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad, wanda mataimakiyar sa Hajjiya Aisha Hamidu,ta wakilta, ya ce ta hanyar wayar da kai ne ɗalibai da matasa za su gane illar amfani da miyagun ƙwayoyi.

A nasa ɓangaren shugaban kungiyar ɗaliban ƴan asaln jihar Kano, da suka shirya taron Abdurrazak Nasiru Ahali, ya ce sun shirya taron ne domin wayar da kan ɗalibai akan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, ta yadda za su kaucewa amfani da su.

Taron faɗakar da ɗaliban illar miyagun kwayoyin yasamu halartar malamai,masu rike da sarautar gargajiya da sauran masana a fannin Ilimi da lafiya.

Continue Reading

Trending