Connect with us

Labarai

Sojoji da ‘yansanda ba sa iya tunkarar yan ta’adda – Tambari Yabo.

Published

on

AIG Tambari Yabo Muhammad mai ritaya ya bayyana cewar yansanda da sojoji basa iya tunkarar surkukin dajin da ‘yan ta’adda da suke.

Tambari Yabo Muhammad ya bayyanawa wakilin gidan radiyon Dala Yusuf Nadabo Ismail hakan ne a birnin sokoto yayin wata ziyarar aiki.

Yabo ya ce a watannin baya ne mazauna kauyuka a jihohin Sokoto da  Zamfara da Katsina suka sha fama da matsalar kashe-kashe, fashi da makami da kuma yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Tambarin ya kuma bayyana cewar zaman da gwamnonin jihohin su kayi a Daura ya taimaka wajen rage yawan matsalar ta’addanci a jihohin.

Ya kuma shawarci gwamnoni jihohin kasar nan da su samar da wata doka wadda za’a baiwa sarakuna da hakimai damar shiga cikin harkokin tsaro, kasancewar sune iyayen kasa.

Daga karshe Tambari Yabo ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kara dagewa wajen dakile matsalar.

Continue Reading
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Labarai

Yadda aka cafke budurwa na kokarin shigar da kwaya gidan gyaran hali na Kano

Published

on

Jami’an gidan gyaran hali na Kurmawa dake nan Kano sun cafke wata budurwa mai suna Zainab Musa ‘yar kimanin shekaru 20 mazauniyar unguwar Hotoro Dan Marke dake nan Kano a yammacin yau.

Ana zargin Zainab Musa da yunkurin shigar da kwaya samfurin Exol har guda 360 acikin miya zuwa gidan gyaran hali na Kurmawa da yammacin yau.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya tattauna da budurwar jim kadan bayan da aka cafke ta inda ta bayyana masa cewa ita ko kadan bata san menene aciki ba, hassalima kawai ta zo gidan gyaran halin ne domin kawowa dan uwanta abinci.

Saidai wani abokin dan uwan nata Mai suna Abdullahi mazaunin unguwar Hotoro, ya ba ta wannan kwanon don ta taho dashi, amma bata san menene aciki ba.

Har ila yau gidan rediyon Dala FM ya ji ta bakin kakakin hukumar gidan gyaran halin ta jihar Kano DSP. Musbahu Lawan Kofar Nassarawa inda ya tabbatar da faruwar al’amarin, ya kuma ce yanzu haka wannan budurwa tana hannunsu kuma suna cigaba da tattara bayanai akai domin su mika ta hannun ‘yan sanda.

Rubutu masu alaka:

Kotu ta aike da wasu matasa gidan gyaran hali

Kotu ta aike da sadiya haruna gidan gyaran hali

Continue Reading

Labarai

Yadda wata mata ta ransa ranta garin zubar da ciki a Kano

Published

on

Yadda wata mata ta ransa ranta garin zubar da ciki a Kano

Wannan al’amari dai ya faru ne a ranar biyar 5 ga watan Mayun shekara ta 2019 da muke ciki, inda wani mutum mai suna Zahraddin Ado ya dauki matar ya kaita gidan wata ma’aikaciyar lafiya mai suna Jummai don ta zubar mata da ciki.

Sai dai a yayin da aka yiwa matar aikin zubar da ciki, a dakin tiyatar da jummai ta bude a gidanta, nan take ta rasa ranta.

A yau ne dai aka gurfanar da wadanda ake zargin a kotun majistiri mai lamba 30 karkashin mai shari’a Yusuf Sulaiman, lauyan gwamnati Barista Lamido Soron dinki ya gabatar da kunshin tuhumar, inda ya bayyana cewar ana zargin su da hada baki da aikata kisan kai.

A karshe dai alkali ya sanya ranar Litinin 18 ga watan da muke ciki domin cigaba da sauraron shari’ar.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il yayi kokarin jin ta bakin lauyan gwamnati amma abun ya ci tura.

Rubutu masu alaka:

BABA SUDA 09 10 2019 Wata mata tayi barin ciki sakamakon dukan da ta sha

Yadda kotu ta wanke matar da ake zargi da kashe mijinta a Kano

Continue Reading

Labarai

Kotu ta yankewa lauyan bogi hukunci a Kano

Published

on

Kotun majistiri mai lamba 35 dake nan Kano, karkashin mai shari’a Sanusi Usman Atana ta yanke hukuncin daurin watanni 20 babu zabin tara ga wani mutum mai suna Prince Ekele.

An gurfanar da Ekele a gaban kotun ne, bisa zargin yana yin sojin gona inda yake yin shigar lauyoyi, sannan yake bi kotuna yana tsayawa masu laifuka da sunan cewa shi lauya ne.

Yayinda ake gabatar da shari’ar Prince Ekele ya amsa laifinsa, inda kotun ta tambayi mai gabatar da kara Nura Mukhtar Funtua kan ko an taba gabatar da Ekele a gaban wata kotu da zargin wani lefi?

A nan ne Nuran ya shaidawa kotun cewar tabbas a kwai tuhumar zamba cikin aminci a kan Ekele cikin kunshin wata kara da wani mutum ya shigar akan cewar ya karbi kudin haya a matsayinsa na lauyansa ya kuma yi uzurin gabansa da kudin har naira miliyan biyu da rabi.

Rubutu masu alaka:

Rashin tsoron Allah ne ke sa yawaitar kisan gilla – Lauya

An halastawa iyaye yi wa yara auren fari-Lauya

Continue Reading

Trending

en_USEnglish
en_USEnglish