Connect with us

Labarai

An cafke wadanda sukayi garkuwa da karamin yaro a Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wani matashi mai suna Anas Isa dan shekaru 22, mazaunin unguwar Zangon Dakata, wanda ake zargida hada baki da kuma sace wani karamin yaro mai suna Abdurrahman Dalha mai kimanin shekaru hudu 4 tare da neman kudin fansa.

Wanda ake zargin ya bayyana cewar wani abokinsa mai suna Sulaiman shi ne ya kawo masa yaron a lokacin da yake tsaka da gudanar da sana’arsa ta aski, domin ya boye shi.

Anas Isa daya daga cikin wadanda ake zargin.

A don haka bayan ya karbi yaron sai ya tafi dashi kauyen Inusawa dake nan Kano gidan wata kanwar mahaifiyarsa mai suna Hajiya Hajjo inda yace da ita yaron ‘dan uwar dakinsa ne suka samu sabani da mijinta shi ne ya kawo shi wurinta domin ta ajiye masa shi, kafin a samu dai-daito.

Daga nan ne kuma suka nemi iyayen yaron da su biya su diyyar zunzurutun kudi har naira miliyyan hudu, sai dai a karshe an dai-daita akan kudi naira miliyan uku.

Rubutu masu alaka:

Yadda aka cafke budurwa na kokarin shigar da kwaya gidan gyaran hali na Kano

Kano9: ‘Yan sanda sun kara ceto yaron Kano daga Onitsha

Amma dai wanda ake zargi Anas Isa ya shiga hannu a yayin da yazo don karbar kudin fansar a yankin unguwar Dakata Bela dake nan Kano.

Wakilin mu Abba Isa Muhammad ya samu zantawa da matar da aka kaiwa ajiyar yaron mai suna Hajiya Hajjo wadda ta bayyana masa cewar ko kadan ba ta san cewa yaron nan sato shi akayi ba, hassalima ita dai dan ‘yar uwarta ne ya kawo mata shi da sunan ‘dan uwar dakin sa ne, amma a karshe ta yi nadama kan aikata wannan laifi na karbar ajiyar yaro ba tare da kwakwkwaran bincike ba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewar a yanzu haka suna cigaba da bincike akai, kuma sun baza komar su domin kamo daya matashin, sannan da zarar sun kammala bincike zasu gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Rubutu masu alaka:

An kara ceto yara biyu da aka sace a Anambra

An ceto rayuwar jamiin kwana kwana da yayi arba da Maikilago

Labarai

Mahukunta ku kawo mana ɗauki a masallacin garin mu – Mazauna garin Ɗan-Dalama

Published

on

Al’ummar garin Ɗan-Dalama da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta kan yadda katangar masallacin Juma’a na garin ta lalace, lamarin da hakan ke barazanar faɗuwar katangar.

Shugaban kwamitin masallacin juma’ar na garin Ɗan Dalama, Mallam Muhammad Mai Nama, ne ya magantu kan al’amarin, inda ya kuma yi kira ga al’umma ciki har da Attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, da su kawo musu ɗauki domin gyara katangar masallacin na Ɗan Dalama, bisa yadda take neman faɗuwa.

Ya kuma ƙara da cewa ba iya katangar ce ke barazanar faɗuwar ba, haka ma cikin masallacin ba a cewa komai, duk kuwa da ƴan kwamitin sun yi bakin ƙokarin su, amma dai kawo yanzu akwai gyare-gyaren da ya ke buƙata.

Continue Reading

Labarai

Ba za’a iya wadata mutane da Fetur ba idan gwamnati ba ta sa hannu ba – Bashir Ɗan Mallam

Published

on

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar man fetur a ƙasar nan, shugaban kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas, ta ƙasa Bashir Ahmad Ɗan malam, ya ce koda kuwa matatar Mai ta Dangote za ta yi ƙarfi ka’in da na’in, ba lallai ne a samu saukin Man fetur ba a ƙasa, matuƙar gwamnatin tarayya bata sa hannu ba.

Bashir Ɗan Malam ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar yau Juma’ar.

Ɗan Mallam ya kuma ce sakamakon yadda gwamnati take taimakawa a fagen shan man, hakan yasa idan har bata sanya hannu ba za’a rinƙa shan wahala wajen samun man fetur ɗin a ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar man fetur, lamarin da ya sa ake siyar da kowacce lita sama da Naira 800 a jihar Kano, inda ake ci gaba da fuskantar manyan layuka a gidajen man da dama.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.

Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.

Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.

Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.

Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.

Continue Reading

Trending