Connect with us

Addini

Duk wanda ya tsere maka a kaunar manzo (s.a.w) ya tsere maka da komai –Limamin Jumu’a

Published

on

A yau jumu’a limamin masallacin jumu’a na Jami’u Ammar bin Yasir dake unguwar Gwazaye a nan Kano, Mallam Abubakar Umar Yasayyadi ya gabatar da huduba akan wajabcin kaunar manzon tsira Annabi (s.a.w).

A yayin da yake gabatar da hudubar ya bayyana cewa ayoyin alkur’ani da hadisan Annabi (s.a.w) duka sun karantar da wajabcin kaunar manzo fiye da iyaye, ‘ya’ya, ‘yan uwa da dangi baki daya.

Wato dai tilas ne mutum ya sanya son manzo fiye da son kowa, kuma hakika duk wanda ya tsere maka a wajen son Manzo (s.a.w) to hakika ya riga da ya tsere maka da komai.

Wakilin mu Abba Isa Muhammad ya rawaito mana cewa limamin yayi kira ga al’umma da su kara zage dantse wajen kaunar manzo ta hakika da kuma koyi da halayensa kyawawa, na hakuri, tausayi da jinkai da kuma karamci.

A wannan watan da muke ciki ne dai musulmai a ko ina a fadin duniya ke gabatar da bukukuwan murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta Annabi (s.a.w) domin nuna kauna a gare shi.

Rubutu masu alaka:

Al’umma na cigaba da raya daren Mauludi a Kano

Kaitsaye: Sheikh Shehu Dahiru Bauchi a Dala FM Kano -Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass 2019

Addini

Matsin Rayuwa: Shugabanni ku sassautawa al’umma – Babban Limamin Kano

Published

on

Babban limamin Kano, kuma wanda ya jagoranci sallar idi a babban masallacin idin na Kofar Mata a nan Kano, Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, ya ja hankalin shugabanni da su sassautawa al’umma, sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, yayi jan hankalin ne yayin huɗubar da ya gabatar, bayan kammala sallar idi da ta gudana a yau Laraba, a babban masallacin idin dake unguwar Kofar Mata a Kano.

Ya kara da cewa kasancewar al’umma na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa, akwai buƙatar shugabanni su yi bakin ƙoƙarin su, domin kawo sauki daga halin matsin halin rayuwar da ake fama dashi.

Yayin sallar Idin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da sauran al’umma da dama ne suka halarta.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Farfesa Muhammed Sani ya kuma ja hankalin al’umma, da su koma ga Allah Subhanahu wata’ala domin samun dacewa a Duniya da gobe Ƙiyama.

Continue Reading

Addini

Ku fara duban watan Sallah daga gobe Litinin – Fadar Sarkin Musulmi

Published

on

Yanzu haka kwamitin ganin wata na Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal, daga gobe Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024 da ake ciki.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a yammacin yau Lahadi a jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

Har ila yau, fadar Sarkin musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar Sarkin musulmin, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito.

Continue Reading

Addini

Iyaye ku kula da tarbiyyar ƴaƴan ku – Malama Fatima Tsakuwa

Published

on

Malamar addinin musulunci dake nan Kano Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta shawarci mata da su ƙara himma wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da kuma zaburar da su mahimmancin yin addu’a a cikin wannan wata na Ramadana, domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T.

Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta bayyana hakan ne yayin taron bita ta musamman da gidauniyar Bango Charity Foundation ƙarƙashin Malama Fatima Yusif Mai tama, wanda gidauniyar ta shirya wa Mata, da bitar ta shafi watan Azumin Ramadana, akan yadda iyaye matan za su kula da ƴaƴan su, da ya gudana a ofishin ƙungiyar dake unguwar Sharaɗa a Kano.

Wakiliyar tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa malama Fatima Tsakuwa ta ce akwai buƙatar iyayen su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma domin rabauta da falala a wajen Allah S.W.T.

Continue Reading

Trending