Connect with us

Rahotonni

Al’umma na cigaba da raya daren Mauludi a Kano

Published

on

Al’ummar musulmi daga ko ina a fadin duniya na cigaba da gabatar da bukukuwan maludi domin murnar zagayowar ranar da aka haifi fiyayyen halitta manzon tsira Annabi (s.a.w), wanda ake yi duk shekara a wannan wata na Rabi’ul Auwal da muke ciki.

Haka abin yake a nan jihar Kano, inda tun kafin shigowar watan al’umma kama daga yara da manya, maza da mata ke ta shirya tarukan mauludi ba dare ba rana a sassa daban-daban na jihar Kano.

Ana kawata wurin Mauludi da kayan ado

Musulmi kan kawata wuraren taron Mauludi da ado kala-kala masu daukar hankali domin girmamawa ga Manzon Allah (s.a.w).

Me ake yi a taron Mauludi?

Musulmai na amfani da taron Mauludi wajen karantar da tarihin manzon tsira Annabi (s.a.w) da kuma koyar da ibadu bisa tsari da tarbiyyar addinin Musulunci.

Haka kuma akan rera kasidun bege, sannan akan baiwa dalibai karatuttuka wanda suke haddacewa su karanto a ranar Mauludi.

Al’umma na yin ankon kayan sawa na musamman domin ranar bikin, haka kuma akan yi girki kala-kala duka dai domin wannan biki.

Ana yin Mauludi ba dare ba rana a Kano

Al’umma na gudanar da bikin mauludi ba dare ba rana a birnin Kano, domin kuwa duk inda ka zaga a lungu da sako na jihar Kano zaka iske al’umma a sassa daban-daban na gudanar da bukuwan na Mauludi.

Gobe Lahadi shi ne dai-dai da ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal ta wannan shekarar, wato dai-dai da ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi (s.a.w), wannan rana tana da matukar muhimmanci ga musulmi.

Addini

Abinda yasa ake hawa dutsen Dala rana Takutaha

Published

on

Hakika hawa dutsen Dala a ranar da ake gabatar da bikin takutaha yana nuna alamun bikin Maguzawa da suke yi a Kano duk shekara, wanda suke hawa dutsen Dala da Gwauron Dutse da Magwan da Fanisau suna gabatar da bukukuwan bauta.

Ganin cewa shi kansa bikin takutaha, malaman Madabo sun qirqire shi ne domin kawar da hankalin matasa da mata daga wadannan bukukuwa na Maguzawa, to da alamun shi ya sa har yanzu a duk ranar bikin takutaha samari da mata da yara suke yin dandazo wajen hawa wannan dutse na Dala.

Duk da cewar su Maguzawa suna gabatar da bautarsu ne bisa jagorancin shugabansu, wato Barbushe wanda yake shiga xakin Tsumburbura ya jiyo musu abin da zai faru a wannan shekarar, kuma ya fito ya sanar da su.

Hoto daga Dutsen Dala a bikin Takutaha na bana

A yanzu ba haka ba ne, domin kuwa sai bayan an gama karatun Madabo kuma babban malami ya yi addu’a an watse. A sannan ne yara da samari suke tafiya domin hawa dutsen Dala. Don haka, ba sharaxin bikin ba ne sai an hau wannan dutsen.

A kan Dala, ana gabatar da abubuwa ne da suka shafi nishaxantarwa da kuma kallon qwaryar birnin Kano. Wasu har hotuna suke xauka. Daga baya, an samu cewar wasu ma suna hawa ne domin su yi shaye-shayen kayan maye da yin caca da kuma faxace-faxacen  ‘yan daba wanda har ta kan kai da ji wa kai rauni. Wannan ba ya rasa nasaba da nason irin yadda maguzawan da suke yin bikinsu a kan dutsen Dalan suke yin shaye-shayen giya da sauransu. Don haka, ana iya kallon wannan gurvacewa a matsayin yadda bikin maguzawan na asali yake a gurvace.

Hoto daga Dutsen Dala a bikin Takutaha na bana

Matsayin Bikin Takutaha

Bikin takutaha muhimmiyar rana ce a cikin garin Kano, domin a wannan rana akan yanke duk wasu hulxoxi a mayar da hankali wajen gudanar da wannan biki, musamman a wajen qananan yara. Dangane da wannan biki kuwa, waxansu suna ganin ba zai rasa alaqa da bautar gunkin Tsumburbura ba, wanda jama’ar Kano suke yi tun kafin zuwan addinin Musulunci (Ibrahim,1982:290). Bukukuwan da Maguzawa suke yi a kan dutsen Dala yana matuqar jan hankalin mata da yara da baqi, don haka sai malaman Madabo suka haxu a masallacin Madabo suka shawarta kan yadda za su xauke hankalin masu zuwa kallon waxannan bukukuwa na Maguzawa.

Manya-manyan malaman wannan zamani da suka zartar da wannan shawara, sun haxa da: Shehu Isa Mai Lawali da Shehu Mamuda mai Mudawwana da Shehu Ibrahim Liman Mai batta da Shehu Sulaiman mai rubutu da sauransu. Haka kuma, an sami wakilcin malamai daga unguwannin Dukurawa da Sheshe da Mandawari da Jujin-‘yanlabu da Maxatai da sauransu (Hassan,1998:97).

Hoto daga Dutsen Dala a bikin Takutaha na bana

Matsayin bikin Takutaha bai wuce ganin an kawar da hankalin yara da mata daga aqidar Maguzanci zuwa tarbiyyar musulunci ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa Madabo suka kafa yin Mauludi a wannan unguwa, wanda daga baya ne mutane suka sauya masa suna zuwa Takutaha.

Dangane da sauran al’umma kuwa, wannan rana tana da matsayi sosai a wajensu. A wannan rana sukan sami damar ziyartar dangi waxanda aka daxe ba a haxu ba. Baya ga haka, qananan yara sukan sami walwala da nishaxi a wannan rana, musamman a kan Dala, inda ake kaxe-kaxe da raye-raye. Har wa yau, masu kayan sayarwa suna samun ciniki sosai, kasancewar jama’a suna zuwa daga vangarori daban-daban. Bugu da qari, al’umma suna haxuwa don yi wa kawunansu da garinsu addu’o’i baki daya.

Rubutu masu alaka:

Fitattun hotuna daga bikin Takutaha na bana

Yadda ake gudanar da bikin Takutaha a Kano

Kun san menene ma’anar  Takutaha?

Marubuci: Tijjani Shehu Almajir

almajir02@yahoo.com

+234(0)8035943092

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,

Jami’ar Bayero, Kano.

Continue Reading

Addini

Fitattun hotuna daga bikin Takutaha na bana

Published

on

Dubunnan musulami ne ke gudanar da bikin zagaye na Takutaha a duk shekara domin tunawa da ranar haihuwar manzon tsira Annabi Muhammad (s.a.w), al’umma na zagaye daga sassa daban-daban na jihar Kano, inda ake zuwa Dutsen Dala.

Masu bikin Takutaha kenan a wani sashe na birnin Kano

Masu bikin Takutaha kenan a wani sashe na birnin Kano

Mallam Sharu Sani Janbulo kenan daya daga cikin Malaman addinin musulunci a Kano.

Masu bikin Takutaha kenan a wani sashe na birnin Kano

Masu bikin Takutaha kenan a wani sashe na birnin Kano

Masu bikin Takutaha kenan a wani sashe na birnin Kano

Masu bikin Takutaha kenan a wani sashe na birnin Kano

Continue Reading

Addini

Yadda ake gudanar da bikin Takutaha a Kano

Published

on

Haqiqa kowane irin al’amari, akwai yadda ake tsara shi kuma a gudanar da shi. Don haka, kowane irin biki a qasar Hausa akwai yadda ake gabatar da shi, wannan ya haxa da yadda ake tsattsara shi daki-daki da kuma irin dokokin da suke tafiyar da shi idan akwai. Bikin takutaha ya qunshi dukkan abubuwan da ake gabatarwa a wannan rana, kama daga karatuttuka da nuna murna ta hanyar nishadi da kuma ziyarce-ziyarcen ‘yan’uwa da abokan arziki.

Karanta: Kun san menene ma’anar  Takutaha?

Karatun Takutaha

A ranar takutaha haqiqa ana gabatar da karatuttuka daban-daban. Tun da sassafe malamai kan taru a cikin masallacin Madabo domin gabatar da wannan karatu. Daga cikin karatuttukan da ake gabatarwa akwai waqoqin yabon Annabi salallahu alaihi wasallam. Yawancin wannan waqoqi ana gabatar da su ne da harshen Larabci. Waqar da aka fi karantawa ita ce, Ishiriniya, sannan akwai kari na musamman wanda sai xan Madabo ne ya iya shi. Haka kuma, a cikin baitukan ishiriniyar, kowane gida a Madabo suna da baitinsu wanda suka zava suka nuna sha’awarsu a kai. Don haka, a duk lokacin da aka zo wannan baiti, akan yi wa shugaban wannan gidan addu’a don tunawa da shi (Hira da M.A.M,11-12-2008).

A duk lokacin da ake gabatar da karatun takutaha, ana ganin abubuwan ta’ajibi, domin akwai wani baiti na ishiriniya wanda da zarar an zo wurin, kowa yana miqewa tsaye, domin malamai sun ce, Manzon Allah salallahu alaihi wasallam yana halartar wurin. A wannan lokaci kuma, takardun ishiriniyar da ke hannun masu karatun, sukan tashi sama suna yawo a kan mutane. Haka kuma, makaru da ke jingine a masallacin kan rabu da qasa su zan yi sama (Hassan, 1998:95).

Hotunan wasu al’umma yayin bikin Takutaha na bana

Bayan karatun ishiriniya, ana gabatar da wasu waqoqin yabon Annabi salallahu alaihi wasallam cikin Larabci kamar haka:

Qasidar isma’uli

Isma’uni aqul                                      ya jami’i, ahlul aqul

Wa madahu hazar Rasul                                  haira min yamdahu Muhammad

Marhaba shahru atana                                   wulida fiha Nabina”

 

Fassarar Hausa

“ku saurare ni zan ambata                             ya jama’a ma’abota ambato

Yabon wannan Annabi                                               shi ne fiyayyen yabo na Annabi Muhammadu

Marhaba da watan da ya zo mana                 A cikinsa ne aka haifi Annabinmu”.

 

Qasidar Muqamul lada

Muqamul lada sudratul muntaha                    Li Ahmadu la shakka fi Mustapha

            Muqamun wa tallahi ma misluhu         Fa wahyun Ilaihi shadidil quwa

           

Lam kallamal Lahu Musa ala              Hamdan la shakka lil Mustapha

            Wa’inna Nabiyyin Abil Qasimu                        Habibur risalati fauqas sama

 

Fassarar Hausa

Muqami mafifici wato sudratul muntaha                     Ga Ahmadu babu shakka tare da Al-Mustapha

Wallahi babu wani muqami ya wannan                       wahayi ne daga Allah mai cikakken mulki.

 

Annabi Musa ya yi magana da Allah               godiya, babu shakka ga Al-Mustapha

Haqiqa Annabi baban Alqasim                                    Masoyin saqo daga Allah.

 

Qasidar Ahlan bi shahril Maulidi

          “Ahlan bi shahrul Maulidi                   Shahrul Nabiy Muhammadi

            Huwa bi sa’adil as’adi                        Khairil Wara Muhammadi”

 

Fassarar Hausa

Marhaba da watan Maulidi                 Watan Annabinmu Muhammadu

            Shi ne Mafificin masu xaukaka                        Mafi alhairin Al’umma Annabi Muhammadu”.

Sannan akwai sauran qasidu da dama kamar su: Qasidar iza raka’a zamanu da Rafa’atul Umuri da Asiru zunubi da Xanxarani da Shahrul rabi’i da sauransu.

Rubutu masu alaka:

Duk wanda ya tsere maka a kaunar manzo (s.a.w) ya tsere maka da komai –Limamin Jumu’a

Al’umma na cigaba da raya daren Mauludi a Kano

Marubuci: Tijjani Shehu Almajir

almajir02@yahoo.com

+234(0)8035943092

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,

Jami’ar Bayero, Kano.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish