Connect with us

Labarai

Kai tsaye: An dage cigaba da sauraron karar Abba da Ganduje

Published

on

Kotun daukaka kara dake zamanta a kaduna karkashin alkalai 5 ta kammala sauraron Dalilan daukaka karar Jam iyyar PDP da dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam iyyar Abba kabir yusuf wadanda suke kalubalantar nasarar da kotun karbar korafe korafen zaben kano ta bawa Abdullahi umar Ganduje na Jam iyyar APC

A zaman kotun na yau lauyoyin hukumar zabe da karkashin J B Dawood SAN sun roki kotun da ta kori daukaka karar sakamakon kura-kurai da suka ce an yi a yayin shigar.

Lauyan Jam iyyar APC Barrister Effiong Effiong ya bayyana cewar basu da suka akan rokon da hukumar zaben tayi harma yace shi bai ga wata gamsasshiyr hujja da zata sanya a daukaka kara a hukuncin da mai shari’a Halima shamaki tayi wanda ta kori karar da PDP ta shigar bisa rashin gamsassun hujjoji ba.

Sai dai lauyan Jam iyyar PDP Adebayo Owomolo ya bayyana  cewar dalilansu na daukaka kara sahihai ne harma ya karanta wata takarda mai kunshe da sadara 9 ya kuma karanta wata takardar mai kunshe da sadara 11 wanda yake bayyana cewar suna da hujjojin daukaka kara

Har ila yau, Barrister Owomolo ya kuma roki kotun da ta rushe hukuncin Justice shamaki an kuma dage zaman dan yin hukunci.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da lauyan Abba Barrister Bashir Muhd Tudun-wuzirci

Shima lauyan Ganduje barrister Ma’aruf Muhammad Yakasai ya yi martani

Labarai

An kama wani matashi da zargin sacewa almajirai kayan sawa

Published

on

Shugaban kungiyar Bijilante na yankin unguwar Hausawa dake karamar hukumar Tarauni a Kano, Usaini Haruna Kailo, ya shawarci iyaye da su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su domin rayuwar su ta zama abar koyi a nan duniya dama ranar gobe kiyama.

Usaini Kailo ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, bayan kama wani matashi da su ka yi, da zargin diban kayayyakin sawa na almajirai cikin wata makarantar tsangaya a unguwar Hausawa ‘yan babura.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyar ya’yan su babu shakka za a rage yawaitar samun lalacewar su”.

Da yake nasa jawabin matashin da a ka kama ya ce” Wannan shi ne na farko kuma shi ne na karshe ba zan kara satar kayayyakin mutane ba”.

Wakilin na mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewa, Kwamandan Bijilanten Usaini Haruna Kailo ya ce, za su mika matashin da su ka kama wajen jami’an tsaro domin matakin da ya dace a kan sa domin hakan ya zama izina ga sauran matasa.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish