Connect with us

Labarai

Kai tsaye :Ana tsaka da fafatawa tsakanin lauyoyi

Published

on

Tuni kotun daukaka kara dake zamanta a kaduna karkashin alkalai 5 ta zauna domin fara sauraron daukaka karar da Jam iyyar PDP da dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar Abba kabir Yusuf suka shigar.

Inda suke rokon kotun da ta rushe hukuncin da mai Sharia Halima Shamaki tayi, wanda ta ayyana Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shekarar 2019 sakamakon rashin gamsassun hujoji da masu kara suka gaza gabatarwa kamar yanda kotun ta ayyana.

A zaman kotun da ake yi a daidai wannan lokaci lauyoyin hukumar zabe da suka hadar da J B Dawood da A A Raji da Abdulkarim Maude sunyi suka akan yanda aka shigar da karar.

Barrister Dawood ya bayyanawa kotun cewar suna suka akan dalilan daukaka karar.

Hukumar zaben ta bakin lauyoyinta sunyi suka akan dalilai na 1 da 2 na da da na 3 da 8 da 13 da 14 da 15 da 16 da 17da dalili na 18.

Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar PDP kenan a harabar kotun daukaka kara dake Kaduna

Barrister Dawood ya bukaci kotun tayi nazari akan wadannan dalilai ya kuma roki kotun da ta kori daukaka karar sakamakon rashin ingancin dalilan masu daukaka kara

Yayin da yake maida martani lauyan Jam’iyyar PDP Barrister Adebayo Awomolo ya bayyana cewar dalilan daukaka karar suna da inganci.

Magoya bayan jam’iyyar APC a harabar kotun daukaka kara dake Kaduna

Harma ya karanta kunshin wata takarda mai dauke da sadarori 9 ya kuma karanta wata takardar mai kunshe da sadarori 11 wadanda yake bayyana ingancin dalilansu na daukaka karar.

Sai dai lauyan Ganduje Effiong Effiong shima yayi suka akan dalilan daukaka karar inda ya ayyana cewar masu daukaka kara basu da wani dalili na daukaka kara dan haka kotun ta kori daukaka karar.

Labarai

An kama wani matashi da zargin sacewa almajirai kayan sawa

Published

on

Shugaban kungiyar Bijilante na yankin unguwar Hausawa dake karamar hukumar Tarauni a Kano, Usaini Haruna Kailo, ya shawarci iyaye da su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su domin rayuwar su ta zama abar koyi a nan duniya dama ranar gobe kiyama.

Usaini Kailo ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, bayan kama wani matashi da su ka yi, da zargin diban kayayyakin sawa na almajirai cikin wata makarantar tsangaya a unguwar Hausawa ‘yan babura.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyar ya’yan su babu shakka za a rage yawaitar samun lalacewar su”.

Da yake nasa jawabin matashin da a ka kama ya ce” Wannan shi ne na farko kuma shi ne na karshe ba zan kara satar kayayyakin mutane ba”.

Wakilin na mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewa, Kwamandan Bijilanten Usaini Haruna Kailo ya ce, za su mika matashin da su ka kama wajen jami’an tsaro domin matakin da ya dace a kan sa domin hakan ya zama izina ga sauran matasa.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish