Connect with us

Labarai

Kai tsaye: Yadda shari’ar Abba da Ganduje ke gudana yanzu haka a Kaduna

Published

on

09:35am

A dai-dai wannan lokaci alkalan kotun daukaka kara dake Kaduna suna gab da zaunawa domin fara sauraron daukaka karar da dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya shigar yana kalubalantar hukuncin da mai shari’a Halima Shamaki tayi a ranar 2 ga watan Oktoban da ya gabata.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Hon. Abdullahi Abbas kenan a harabar kotun.

Kotun sauraron kararrakin zabe ta kori karar da Abba Kabir ya shigar inda ta bayyana Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben sakamakon rashin gamsassun shaidu kamar yadda kotun ta bayyana a baya.

Dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Kwamaret Aminu Abdussalam, da kuma shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano Hon. Rabi’u Sulaiman Bichi, da kuma Hon. Shehu M. Bello shugaban Kwankwasiyya Movement na jihar Jigawa, a harabar kotun.

A yau ne dai kotun daukaka kara dake Kaduna zata saurari kowane bangare daga nan kuma ta sanya ranar yin hukunci, wakilinmu Yusuf Nadabo Ismai’l ya bayyana cewar tun da misalin karfe 7:30 na safe magoya bayan Jam iyyar APC dana PDP Sun cika harabar kotun, an kuma jibge jami’an tsaro kewaye da kotun daukaka karar.

Rubutu masu alaka:

Kotu ta tsayar da ranar raba gardama tsakanin Ganduje da Abba

Kotu ta tsayar da ranar raba gardama tsakanin Ganduje da Abba

Continue Reading

Labarai

Kotu zata yanke hukunci kan tsofafin shugabannin karamar hukumar Warawa

Published

on

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan tsofafin shugabannin karamar hukumar Warawa da ake zargi da aikata ba dai-dai ba.

Kotun majistret mai lamba 15 karkashin mai Sharia Muntari Garba Dandago ta sanya ranar 16 ga watan gobe dan zartas da hukunci a kunshin tuhumar da ‘yansanda suke yiwa tsofafin shugabaninn karamar hukumar Warawa.

Wadand ake tuhuma sun hada  Ibrahim Abdullahi da Shehu Shazali wadanda ake zargi da lefin hada baki da yunkurin tayar da hankali da kuma lefin buga takardun jabu dangane da gonakin manoma na yankin katarkawa.

Wajibi ne bin umarnin kotu idan har ta bayar da umarni- Lauya

Kotu ta dakatar da Ganduje daga sabuwar dokar majalisar masarautar Kano

Buhari yayi nasara a kotun Koli.

wakilin mu  Yusuf Nadabo ya rawaito cewar, sai dai a yayin da ake karanta kunshin tuhumar dukkanin su, sun musanta zargin.

 

Continue Reading

Labarai

Ana zargin matashi da aikata kisan kai

Published

on

Kotun majistret mai lamba 58 karkashin mai shari’a Zubairu Inuwa ta aike da wani matashi gidan gyaran hali.

‘yan sanda sun gurfanar da matashin mai suna Felix Abah wanda ake tuhumar sa da aikata kisan kai.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar tun a ranar 6/4/2017 Felix ya gayyaci wani mai koyar da tukin mota mai suna Sani Abbas dan ya koya masa mota, amma daga karshe sai ya hallakashi ya gudu da motar ya sayar da ita miliyan daya da dubu dari bakwai.

A karshe kuma ya mika kansa caji ofis yayi ikirari a gaban ‘yansanda cewar shine ya hallaka Sani.

Kotun ta sanya ranar 10/1/2020 dan jiran shawararar lauyoyin gwamnati.

Wakilinmu yusuf Nadabo Ismail ya zanta da mahaifiyar Sani wadda tace tun lokacin da aka kashe sani bata da kwanciyar hankali.

Shima Felix ya bayyana cewar ya mika kansa caji ofis ne sakamakon rashin nutsuwar da ya shiga tun lokacin da yayi kisan.

Continue Reading

Labarai

DW ta baiwa Freedom Radio sabbin Babura don inganta ayyukansu

Published

on

Shugaban sashin hausa na gidan radion DW Thomas Mosh, ya ce kyautata alaka tsakanin kafafen yada labarai na duniya zai kawo cigaba ta fannin aikin jarida.

Thomas Mosh, ya bayana hakan ne lokacin da yake mika makullin babura masu kafa biyu, guda hudu ga janar manajan gungun rukunin tashoshin Freedom Radio da yammacin Yau alhamis, a shelkwatar Freedom Radio dake unguwar Sharada a birnin Kano.

Moshe, ya kara da cewar DW ta bayar da baburan ne ga Freedom Radiyo Kaduna dan kara zaburar da ma’aikatanta musamman sashin wasanni.

Da yake nasa jawabin bayan karbar baburan janar manaja, na Freedom Radio Malam Adamu Isma’ila Garki, cewa yayi hakan zai kara inganta aikin tashar kasancewar dama akwai yarjejeniyar aiki tare.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa hukumar gudanarwa ta Freedom Radio da Dala Fm Kano sun mika Kyauta ga shugaban sashin hausan na tashar DW, haka kuma shugaban tashar Freedom Radio Kano Malam Ado Saidu Warawa, da na Dala Fm Kano Ahmad Garzali Yakubu, da sauran shugabanni na daga cikin wadanda suka kasance a gurin taron.

 

Continue Reading

Trending

en_USEnglish
en_USEnglish