Connect with us

Manyan Labarai

Yawan wadanda hukuncin kisa ya hau kansu na karuwa.

Published

on

Sakamkon rashin gaggauta zartas da hukuncin kisa akan lokaci, hukumomin gidajen gyaran hali a Najeriya na kokawa da yawaitar wadanda hukuncin ya rataya a wuyan su a Jarum.

Cikin shirin shari’a a aikace dake gudana a wannan tasha da karfe 9 na safiyar litinin zuwa Alhamis, kakakin gidan gyaran hali DSC Musbahu Lawan ya bayyana cewar yanzu haka gidajen dake jihar kano sun cika da masu jiran hukuncin kotuna akan manyan laifuka da suka aikata.

Musbahu Lawan ya kara da cewa yawan wadannan rukuni na masu jiran hukuncin kisa sun kai 130 a watanni 3 da suka gabata, yayin da a yanzu yawansu ke karuwa a kullum.

Kakakin hukumar ya roki gwamnatin jihar kano ta sanya hannu wajen zartas da hukuncin da kotuna suka yankewa wadannan rukuni cikin gaggawa, domin rage yawaitar su a kurkukun Kurmawa.

Wakilin mu Abubakar Sabo da ya jagoranci gabatar da shirin ya bamu labarin cewar kakakin hukumar yace ruwan gwamnayi ta sanya hannun a zartas musu da hukuncin da kotu yanke musu, ko kuma ta saukaka musu kan hukuncin dauri na shekaru, ko kuma ta sanya hannun sakin su, musamman wadanda ake ganin alamun nagarta a tattare dasu, sakamakon dadewa da suka yi a wannan gida.

Ya kara da cewa yanzu haka wasun su har tsufa ya fara cimmusu, tsawon shekarun da suka shafe suna zaman jiran hukunci.

Wannan dai shine karo na biyu da hukumar gidajen gyaran hali a kano ta koka kan jan kafa da gwamnati keyi wajen tabbatar da hukuncin da kotuna suka yankewa masu laifuka da suka shafi kisa da makamantansu, inda watanni 3 da suka gabata ma dai hukumar tayi jankalin yawaitar wadanda kotuna ke aiko musu domin kashewa.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kai tsaye: Ma’anar bikin Maukibi da akeyi yau a Kano

Published

on

Ku cigaba da bibiyar wannan shafi domin ana cigaba da sabinta shi.

(more…)

Continue Reading

Manyan Labarai

KAROTA zata sanya kafar wando daya da masu Adaidaita sahu -Baffa Babba

Published

on

Gwamnatin Kano tace duk mai tuka babur mai kafa Uku da yake ganin yafi karfin doka to Ya jira zuwa lokacin da za a rufe yin rajistar masu Adaidaita Sahu, yaga yadda za su kwashi Yan kallo da jami’an Karota matukar ya hau titin Gwamnati.

Shugaban hukumar karota Baffa Babba Dan Agundi, ya bayana hakan yayin taron manema Labarai da ya gudana yau a shelkwatar karota dake  nan Kano.

Dan Gundi, ya kara da cewar tsarin da Gwamnatin Kano ta fito dashi ya zama wajibi don inganta harkokin tsaro da kuma sanin masu gudanar ta sana’ar Tuka Adaidaita Sahu a jihar Kano.

Ba zamu ragawa yan adaidaita sahu ba -KAROTA

Dambarwa ta barke tsakanin masu lodin ababan hawa da KAROTA

An dage cigaba da sauraron karar shugaban KAROTA

Baffa Babba Dan Agundi, ya kuma kara da cewa Gwamnati bata yanke ka’idar abunda za a karba daga gurin masu babura mai kafa uku ba saida ta zauna da shugabannin kungiyoyin su wanda sune ma suka yanke abunda za a karba daga garesu.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewar Baffan bai amsa tambaya daga manema labarai ba game da karancin fitowar jami’an na Karota kamar yadda aka saba ganinsu ba a yau, yayin da ofishin KAROTA ya kasance a zagaye da jami’an ‘yansanda don tabbatar da doka da orda.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Kotu zata yanke hukunci kan tsofafin shugabannin karamar hukumar Warawa

Published

on

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan tsofafin shugabannin karamar hukumar Warawa da ake zargi da aikata ba dai-dai ba.

Kotun majistret mai lamba 15 karkashin mai Sharia Muntari Garba Dandago ta sanya ranar 16 ga watan gobe dan zartas da hukunci a kunshin tuhumar da ‘yansanda suke yiwa tsofafin shugabaninn karamar hukumar Warawa.

Wadand ake tuhuma sun hada  Ibrahim Abdullahi da Shehu Shazali wadanda ake zargi da lefin hada baki da yunkurin tayar da hankali da kuma lefin buga takardun jabu dangane da gonakin manoma na yankin katarkawa.

Wajibi ne bin umarnin kotu idan har ta bayar da umarni- Lauya

Kotu ta dakatar da Ganduje daga sabuwar dokar majalisar masarautar Kano

Buhari yayi nasara a kotun Koli.

wakilin mu  Yusuf Nadabo ya rawaito cewar, sai dai a yayin da ake karanta kunshin tuhumar dukkanin su, sun musanta zargin.

 

Continue Reading

Trending

en_USEnglish
en_USEnglish