Connect with us

Addini

Zagin shugabanni ya sabawa koyarwar addini – Dakta Abdallah

Published

on

Limamin Masallacin Juma’a na Usman Bin Affan dake Gadon Kaya Dakta Abdallah Usman Umar, ya shawarci al’ummar musulmi da su kaucewa zagin shugabanni a yayin da shugabannin su ka yi musu laifi.

Dakta Abdallah Usman ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowa daga cikin shirin Rayuwa Abar Koyi wanda ya gudana a gidan Rediyon Dala da safiyar yau Juma’a, yana mai cewa zagin shugabannin ya saba da koyarwar addinin musulunci

Ya kuma ce zagin shugabannin da wasu daga cikin Al’umma keyi ka iya lalata jagorancin nasu maimakon gyaruwa wanda hakan zai shafi dukkanin al’aumma.

Wakiliyar mu Rukayya Mika’ilu ta rawaito cewa, Dakta Abdallah, ya ce su ma shugabanin wajibinsu ne su kiyaye abun da zaisa mutane sun dinga zarginsu ko kuma su riga ganin cewa sun aikata ba daidai ba.

 

Continue Reading

Addini

Kai tsaye: Ma’anar bikin Maukibi da akeyi yau a Kano

Published

on

Ku cigaba da bibiyar wannan shafi domin ana cigaba da sabinta shi.

(more…)

Continue Reading

Addini

Muna goyon bayan Dahiru Bauchi kan raba masarautar Kano- Shaik Al-kadiri

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Kurna layin gidan kara kuma shugaban kwamitin koli na Azzawiyal kadiriyyar Aliya shaik Jamilu Alkadiri Fagge ya bayyana goyon bayansu ga jawaban shaik Dahiru Usman Bauchi wanda ya shawarci gwamnan Kano Dr, Abdullahi Ganduje da ya sauya tunani dangane da rarraba masarautar Kano.

Khudibar limamin a yau ta mayar da hankali ne akan gwaggwaban ladan da masu koyi da kaunar fiyayyen haliita Annabi Muhammad suke samu dare da rana .

Sai dai malamin yayi tsokaci akan batun raraba masarauta inda ya bayyana cewar daukacin al’ummar dake zawiyarsu dama ragowar ‘yan uwa duka basa tare da wannan sabuwar doka ya kuma bayyana cewar sun zauna da mai girma gwamna su kimanin 10 sun kuma shawar ce shi da abar wannan magana sakamakon illar da zatayiwa ga addini da kyawawan al’adun Kanawa.

Majalisar shura ta Tijjaniyya bata goyan bayan raba masarautar Kano- Mai hula

Kurunkus: Ganduje ya rattaba hannu kan kudurin rarraba masarautar Kano

Shaik Alkadiri ya bayyana cewar kasancewar ana kiran mai girma gwamna da sunan khadimul Islam watakila ko dan taimakon addini da yake yi to amma ya shawarci gwamnan da ya duba wannan batu kasancewar sabuwar dokar rarraba masarauta zai haifar da rashin zumunci da rarrabuwar kawunan al’uumma

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya uwaito cewar limamin ya karanta Surorin Falaki a raka ar farko yayin  ta biyu ya karanta Nas’i

Continue Reading

Addini

Majalisar shura ta Tijjaniyya bata goyan bayan raba masarautar Kano- Mai hula

Published

on

Shugaban majalisar shura ta darikar Tijjaniyya Halifa Sani Shehu Mai hula ya ce darikar Tijjaniyya bata goyon bayan taba masarautar Kano wanda gwamnatin Kanon take yi a halin yanzu.

Halifa Sani Shehu me Hula ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai wanda ya gudana da safiyar Alhamis din nan a nan Kano.

Ya kuma Kara da cewa tun a baya sun zauna da gwamnati da kuma masarautar suka kuma bada shawarwari amma kuma aka ki amfani da shawarar aka ci gaba da taba masarautar don haka ne ya zamar musu dole su bayyana matsayar su akai kamar yadda shima sheik Dahiru Usman Bauchi ya riga ya yi bayani.

Darikar tijjaniyya ta ce ba ta goyon bayan taba masarautar Kano

Raba Masarautar Kano: Umarnin kotu baizo mana akan lokaci ba -Sakataren gwamnatin Kano

Gwamnati za ta kashe masarautar Kano- Farfesa Naniya

Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa Halifa Shehu Sani mai Hula ya kuma ce wannan Ita ce matsayar da dukkanin mabiya darikar Tijjaniya suke kai.

 

 

Continue Reading

Trending

en_USEnglish
en_USEnglish