Connect with us

Ilimi

Kazanta da rashin kula da kai shi ke janyo sankarar mama – Saudat Sani

Published

on

Shugabar kungiyar tsaffin daliban makarantar sakandiren kwana ta ‘yanmata dake Dala Hajiya Saudat Sani, ta ce kazanta da kuma rashin sanin yadda ‘yanmata a makarantun kwana za su kula da kansu, shi ne ke jawo musu kamuwa da cutur sankara dama sauran cututtukan mata tun suna ‘yan mata.

Hajiya Saudat Sani ta bayyana hakanne a ganawarsu da gidan radiyon Dala da safiyar yau, lokacin da take tsokaci kan kalubalen tsafta a makarantun kwana na mata.

Ta kuma ce matukar daliban suka dauki matakan kariya, to za’a samu raguwar cututtukan mata a tsakanin al’umma.

Saudat Sani ta kuma kara da cewa wannan dalili ne ya sanya kungiyar shirya wani taron wayar da kan daliban don ganin sun dauki matakan kaucewa kamuwa da cututtukan.

Wakiliyarmu Maryam Abubakar ta rawaito cewa shugabar kungiyar daliban ta kuma bukaci gwamnati data kara mai da hankali wajen samar da isassun kayayyakin kula da tsaftar mata a makarantun, tare da kulawa ta musamman daga bangaren iyaye domin ganin an magance matsalar baki daya.

Ilimi

Covid-19: Gwamnati za ta fitar da tsarin bude makarantu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shiri ya yi nisa wajen ganin an bude makarantu domin cigaba da harkokin neman ilimi a fadin kasar nan, tun bayan rufe su da a ka yi sanadiyyar annobar Corona.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya sanar da hakan inda ya ce nan bada jimawa ba, gwamnatin za ta fitar da tsarin bude makarantun, ba tare yaduwar cutar ba.

Ya kuma ce “Yanzu haka ma’aikatar ilimi da kwamitin fadar shugaban kasa na duba hanyoyin bude makarantun cikin aminci. Matakin rufe makarantun an yi shine domin dakile yaduwar cutar a fadin kasa”. A cewar Boss.

Continue Reading

Ilimi

Covid-19: An baiwa ‘yan Jaridu horo kan Corona a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta cigaba da baiwa ‘yan jaridu goyon baya musamman a kan kare kansu daga cutar Corona yayin gudanar da ayyukan su.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yau Asabar lokacin gudanar da taron bita ga ‘yan Jaridu a kan yadda za su kare kansu daga kamuwa daga Corona yayin gudanar da ayyukan su.

Ya ce” ‘Yan jaridu su na taimakawa a wannan yaki da a ke yi da wannan cuta, domin haka ya zama lallai su samu kariya daga kamuwa daga samun cutar”. Ganduje.

Da yake jawabi shugaban kwamitin gwamnatin a kan cutar Corona a Kano na gwamnatin tarayya, Dr Nasir Sani Gwarzo cewa ya yi” Kasancewar ‘yan jaridu na cikin hatsarin kamuwa da cutar, domin haka ya zama lallai a ilmantar dasu yadda za su kare kansu”. Dr Nasir.

Abbas Ibrahim shi ne shugaban kungiyar ‘yan jaridu reshen Kano ya ce” Wannan horarswar za ta taimakawa ‘yan jaridun wajen yin ayyukan su cikin kariya”. Kwamrade Abbas.

Wakiliyar mu a fadar Gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta rawaito cewa jami’an lafiya daga fannoni daban-daban ne su ka yi ta gudanar da mukalolin kariyar ‘yan jaridu daga cutar ta Covid 19.

Continue Reading

Ilimi

Gwamnati ta rinka taimakawa dalibai masu bukata ta musamman – Ibrahim Isma’il

Published

on

Mataimakin shugaban tsofaffin daliban makarantar Tudun Maliki bangaren masu lalurar gani Ibrahim Isma’il Abdullahi, ya bukaci gwamnatin jiha da ta ringa bawa masu bukata ta musamman guraben aiki, kamar yadda ake baiwa sauran al’umma.

Ibrahim Isma’il ya bayyana hakanne a zantawarsu da gidan rediyon Dala da safiyar yau.

Ya na mai cewa, duk abinda aka tanada domin masu bukata ta musamman a kowanne rukuni a basu, domin acikinsu akwai masu ilimi da zasu iya tafiyar da wannan bangare.

A nasa jawabin mai Magana da yawun kungiyar Hamza Aminu Fagge, ya ce suna tara kudi a junansu domin tallafawa wasu suma su samun ilimi.

Wakilinmu Buhari Isah, ya rawaito cewa, masu bukata ta musamman sun yi kira ga sauran masu bukata ta musamman da su hada kansu domin zama a inuwa daya su samarwa kansu cigaba.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish