Labarai
Wani malamin jami’a ya samu gurbi a gidan yari
Kotun majistret mai zamanta a Rijiyar Zaki ta aike da wani malamin jami’a gidan gyaran hali bisa zargin bata suna da cin mutunci.
Tun da farko ‘yan sanda ne suka gurfanar da wannan lakcara mai suna Mustafa Hashim Kurfi wanda wani mai suna Abba Musa yayi korafi akansa.
Kunshin tuhumar ya bayyana cewar Abban ya yi korafin cewar lakcaran ya duddura masa ashariya shi da ‘yan uwansa ta wayar tarho harma Abban ya nadi muryar malamin lokacin da yake yin ashar din.
Sai dai wanda ake zargin wato malam Mustafa Hashim Kurfi ya musanta zargin.
Barista Ma’aruf Muhammad Yakasai shine lauyan da yake kare Mustafa Hashim ya kuma roki kotun da ta sanya shi a hannun beli kasancewar akwai dangantakar auratayya tsakanin mai kara da wanda ake kara.
Sai dai mai gabatar da kara Yusuf Saleh ya yi suka inda yace bayar da belin Mustafan zai haifar da tarnaki ga binciken ‘yan sanda.
Mai Shari’a Aminu Usman Fagge ya sanya ranar 19 ga wannan watan dan bayyana matsayar kotun.
Labarai
NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya
Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.
“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.
Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.
Labarai
Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu
Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.
Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.
Labarai
Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya
Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.
A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.
Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.
Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su