Connect with us

Manyan Labarai

Sarkin Kano ya maka hukumar karbar korafe-korafe ta Kano a gaban kotu

Published

on

Babbar kotun jIha mai lamba 10 karkashin jagorancin mai shari’a Sulaiman Baba na malam ta sanya ranar 30 ga watannan da muke ciki don cigaba da shariar nan wadda sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na II ya shigar gabatan .

Malam Muhammad Sanusi na kalubalantar rahoton hukumar karbar korafe-korafe ta jihar kano wadda ta fitar da rahoton cewa a kaddamar da bincike akan sarkin tun a kwanakin baya.

Haka zalika Sarkin na Kano ta bakin lauyansa Barrister Abubakar Balarabe Mahamud mai darajar SAN ya bayyanawa kotun cewar, ba a bashi damar kare kansa ba kafin fitar da rahoton don haka ya roki kotun da ta rushe sakamakon binciken tun da dai an tauye masa damar da kundin tsarin mulki ya bashi.


A zaman kotun na yau Alhamis lauyoyin masu kara sun bayyana cewar, akwai tasgaro a ra’ayin kotun da ta fara sauraron shari’ar dangane da rokon da suka yi na bada umarnin sashirari wadda kotun baya taki cewa komai akan rokon, Kuma Sharia irin wannan bata yiwuwa sai an samu wannan umarni.

Ganduje ya nada sarkin Kano shugaban majilisar sarakuna

Ganduje ya bada umarni a gyara gidan shattima

Majalisar shura ta Tijjaniyya bata goyan bayan raba masarautar Kano- Mai hula
Daga bisani mai shari’a Namalam ya dage zaman sauraran shari’ar zuwa ranar 30 ga wannan watan da muke ciki na Janairu.
Cikin wadanda akayi kara sun hadar da gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje da kwamishinan Sharia

Labarai

Rahoto: hukumar NDLEA na hukunta duk jami’in ta da ya yi laifi – Dakta Ibrahim Abdul

Published

on

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kasa reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul ya ce, duk lokacin da ya samu daya daga cikin ma’aikatan su ya yi laifi, ya na hanzarin daukar matakin kora ko kuma hukuncin da ya dace.

Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, lokacin da yake mayar da martani a kan matasan da a ke zargin sun fada ruwan kududdufi lokacin da hukumar ta NDLEA ta kai simame yankin Dan Agundi da ke jihar Kano.

 

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa 2 sun gurfana a kotu kan zargin raunata jami’an KAROTA 3

Published

on

Kotu mai lamba 47, da ke rukunin kotunan majistret a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Huda Haruna Abdu, wasu matasa biyu Yunusa Sunusi da kuma Muhammad Babagana, sun gurfana a kotun da tuhumar a kan yi wa wasu jami’an hukumar KAROTA rotse, da suka hada da Usamatu Abdullahi da Sulaiman Musa da kuma Abdulkadir Isma’il.

Ana tuhumar matasan da laifuka guda uku, laifin hada baki da cin zarafi da kuma haddasa mummunan rauni, laifukan da suka saba da sashi na 93 da sashi na 264, sai kuma 247 na kundin laifuka, bayan kuma an karanta musu kunshin tuhumar zargin da a ke yi musu duk sun musanta.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotu ta fara sauraren shari’ar matar da a ke zargi da kazafin maita

Published

on

Wata mata ta gurfana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola a kan zargin bin gari tana yada labarin cewa makwabciyarta da ‘ya’yanta duk mayu ne.

Tun da fari dai matar da a ke zargi da maitar, ta garzaya ofishin ‘yan sanda, tana karar makwabciyar tata, daga bisani kuma ‘yan sanda su ka tattara bayanai su ka mika su kotu domin fara sauraran shari’ar, bayan kuma karantawa matar mai yada labarin maita kunshin tuhumar ta musanta, inda kotu ta dage sauraren shari’ar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!