Manyan Labarai
Hana zancen dare zai rage badala tsakanin samari da ‘yan mata-Hukumar shari’a
Hukumar shari’ar muslunci ta karamar hukumar Warawa, ta nemi gwamnatin jihar Kano da kuma hukumar Shari’ar musulunci ta jiha, da ta yi dokar hana zancen dare a tsakankanin samari da ‘yan mata na jihar Kano sakamakon badala da ta ke faruwa a tsakantsakin matasa’
Shugaban hukumar na yankin, Isma’il Yusuf Tafida ne, ya bayyana hakan a yayin taron limaman kananan hukumomin Warawa da Dawakin Kudu wanda sashin yada addinin musulunci na hukumar shari’ar musulunci ta jihar Kano ta gudanar a karamar hukumar Dawakin Kudu.
Ya ce” matsalar da zancen dare ke haifarwa a yanzu musamman ma yada badala a da gwamnatin jihar Kano za ta hana zancen da tuni an samu sauki”.
Ya kuma ce” in har ya zama wajibi sai an yi zancen da a rinka hadawa da dan rakiya domin ganin an kamala zancen a gaban sa gudun ka da shedan ya shiga tsakanin samari da ‘yan mata. Idan aka duba yadda zamanin baya yake ai bah aka ake yin zance ba a tsakanin samari da ‘yan mata”. A cewar Isma’ila Yusuf Tafida.
Sannan ya kuma ce” limamai da su kara karfafa karbar shaidar gwajin lafiya kafin daura aure, sabida gwajin lafiyar yana da amfani gudun kada a daura aure tsakanin mai lafiya da kuma mai dauke da cuta”.
Hangen Dala
Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano
A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.
Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.
Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.
Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.
Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.
Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito
Manyan Labarai
Jam’iyyar NNPP ta dakatar da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf
Tsagin jam’iyyar NNPP ta ƙasa karkashin jagorancin Major Agbo, ya sanar da dakatar da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf daga cikin jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar ta ƙasa Ogini Olaposi, ya fitar a yayin taron ‘yan jarida a Talatar nan a Abuja, tsagin jam’iyyar ta NNPP, ya ce rashin bayyana a gaban kwamitin ladabtarwar jam’iyyar da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi shine ya sanya su ɗaukar wannan mataki.
Ya ƙara da cewa matakin na zuwa ne sakamakon fusata da jam’iyyar ta yi kan halartar wani babban taron jam’iyyar da gwamnan ya yi wanda tsagin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya jagoranta a ranar 6 ga watan Afrilun nan na shekarar 2024. kamar yadda jaridar THE PUNCH ta rawaito.
Sai dai tuni wasu ƴan Kwankwasiyyar suka yi watsi da wannan dakatarwa.
Dambarwar dai na zuwa ne yayin da itama jam’iyyar APC, ke ci gaba da fuskantar ta ta dambarwar, musamman ma da aka jiyo yadda wani sashi na shugabancin jam’iyyar a mazaɓar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, aka jiyo shi ya dakatar da shugaban riƙo na APC ta ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, daga cikin jam’iyyar.
Sai dai daga bisani shugabancin jam’iyyar ta APC, a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, ya musanta batun dakatarwar lamarin da yace ma ana shirye-shiryen ɗaukar mataki akan waɗanda suka bayyana dakatarwar.
Manyan Labarai
APC ta dakatar da Dakta Abdullahi Ganduje daga jam’iyyar
Jam’iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar.
Mai bai wa jam’iyyar shawara a ɓangaren shari’a a mazaɓar Ganduje, da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Halliru Gwanzo, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da manema labarai a jihar ta Kano, kamar yadda jaridar online ta Nigerian Triker ta rawaito.
Halliru Gwanzo, ya kuma ce sun ɗauki matakin dakatar da tsohon gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne sakamakon zarge-zargen da gwamnatin jihar Kano take masa a kan yin badaƙala da kuɗin al’ummar jahar.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su