Connect with us

Addini

Bada taimakon Naira 10 a masallatai zai rage talauci ga musulamai- Malam Murtala

Published

on

Hukumar shari’a musulunci ta jihar Kano, ta ce da al’ummar musulmai za su rinka bada taimakon naira 10 a kowane masallacin juma’a da tuni ba a sami yaran da suke tallace-tallace a kan titi da kuma mutanen da suke neman kudin taimako na rashin lafiya a jihar Kano.

Daraktan yada addinin musulunci na hukumar, Muratala Muhammad Adam ne, ya bayyana hakan yayin taron limaman masallatan juma’a wanda ya gudana a karamar hukumar Dawakin Kudu.

Ya ce akwai bukatar al’umma da su rinka amfani da damar su wajen taimakon juna ta hanyar amfani da masallatai.

Ya kuma ce da za a rinka tattara kudaden da ake bayarwa a masallatai da an rinka tallafawa mata suna karatun aikin likita.

Shi kuwa a nasa jawabin yayin taron shugaban hukumar na karamar hukumar Dawakin Kudu,Abdulkarim Husseini Abdulkarim, cewa al’umma da su yi amfani da damar su yun a yanzu.

wakilin mu Tijjani Adamu, ya rawaito cewa taron limaman ya samu halartar limaman masallatan kananan hukumomin Warawa da na Dawakin Kudu.

 

 

 

 

 

 

Addini

Al’umma su kasance masu taimakon juna – Liman

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shalkwatar rundunar ‘yan sanda da ke unguwar Bampai SP Abdulkadir Haruna ya ce, ya kamata mutane su rumgumi dabi’ar taimakon junan su musamman wadanda Allah ya wadata su.

Limamin ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar sallar juma’a da ya gudanar a shalkwatar ‘yan sanda a ranar Juma’a.

Ya na mai cewa, “Idan mutane su ka jikan na kasa da su zai jikan su, sannan kuma tuba ga Allah, na kawo ci gaba da yalwar arziki”. Inji SP Abdulkadir

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta ruwaito cewar, limamin ya kuma ja hankalin mutane da su kara kiyaye wajan aikata laifuka domin Allah ya na jarabtar bayi da masifu idan laifinsu ya yi yawa.

 

 

Continue Reading

Addini

An gudanar da jana’izar ‘dan Shaihu Ibrahim Inyas a Senegal

Published

on

Tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II ya bi sahun dubban al’ummar musulmi wajen gudanar da jana’izar Halifan Tijjaniya kuma ‘Da ga shehu Ibrahim Inyas wato Ahmad Tijjani Inyas da ya rarsu a ranar Talatar da ta gabata.

An dai gudanar da jana’izar shehin malamin ne a yau Juma’a babban masalacin juma’a na shehu Inyas da ke birinin Kaulaha da ke kasar Senegal.

Marigayi Sheikh Khalipa Inyass shi ne ‘Da na hudu a cikin jerin ‘ya’yan Sheikh Ibrahim Inyass.

shi ne kuma Halipan sa na hudu cikin jerin Halifofinsa  tun bayan rasuwar sa a shekarar 1975.

Muhammadu Sunusi jim kadan bayan kammala jana’izar ne ya aike da sakon ta’aziyyar sag a al’ummar musulmi.

“Ina farawa da isar da ta’aziyya ta ga ‘yan uwa masu girma, bisa wannan babban rashi da mu ka yi, kamar yadda ku ka sani, gamu a nan al’umma da dama daga Najeriya sama da dubunnai, wasu daga Abuja, Kano da Legas da kuma sauran garuruwa, muna rokon Allah ya sada Shehin mu da rahamar sa, ya kuma sanya shi a aljannah”. Inji Malam Muhammadu Sunusi II

A watan Yuni ne dai na shekarar 2018 Sheikh Ahmed Inyas ya ziyarci fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da wasu manyan ‘yan Nijeriya, ciki har da Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u.

 

Continue Reading

Addini

Muna kira ga gwamnatin tarayya ta magance matsalar tsaro – CAN

Published

on

Kungiyar kiristoci ta kasa CAN ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen rashin tsaro da kashe-kashen mutane a kudancin jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar reshen jihar Bishop Goddy Okafor ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce, “Rashin tsaro na taka rawa wajen tashin hankula wanda yake sanadiyar kashe mutanen da ba su ji basu-gani ba”.

Ya kuma ce, “Kamata ya yi gwamnatin tarayya ta yi duba na tsaki kan yiwuwar kawo tsaro a jihar da ma kasa baki daya, da nufin inganta harkokin kasa”.

Bishop Goddy ya kara da cewa, “Yawan kisan da a ke samu arewacin kasar ya munana, a don haka gwamnatin tarayya da na gwamnatocin arewacin jihohin kasar nan, su rubanya kokarin su wajen kawo rashin tsaro a kasa”. Inji Biship Goddy

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish