Connect with us

Manyan Labarai

Mun tashi da ganin ana yi wa gidajen mu jan lamba- Al’ummar garin Ajawa

Published

on

Da safiyar Juma’ar nan ne al’ummar garin Ajawa dake karamar hukumar Gwale suka tashi da ganin wasu mutane da suke zargin ma’aikatan hukumar tsara birane na jihar Kano tare da rakiyar  tarin  ma’aikatan tsaro.

Ma’aikatan dai sun tayi  gidajen su jan lambar STOP/KNUPDA.

Wasu daga cikin mutanen yankin sun shaidawa wakilin mu Abubakar sabo cewa jama’an sun yiwa gidaje sama da guda dari biyu Jan lambar l.

Haka zalika ba kuma tare da kasa a gwiwa wakilin na mu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar ta wayar ta fi da gidan wanda ya ce za su bincika.

A wani labarin kuma  masu sayar da kasuwar ne a hauran makaranta suka koka dangane da cewa a Alhamis din nan da ta gabata  wasu mutane suja zo suka auna filin da gwamnatin Kano ta ce za ta basu su cika da sana’wr su ta saida dabbobi a wurin. Sakamakon tashin da aka yi a inda suke shekara da shekaru.

Wakilin my Abubakar sabo ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar ta wayar salula wanda ya ce za su bincika.

Labarai

An yi wa jami’an hukumar makarantun Alkur’ani da Islamiyya bita a kan Corona

Published

on

Shugaban cibiyar bincike kan cututtuka ma su yaduwa ta jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Isah Sadiq Abubakar ya bukaci al’umma su ci gaba da amfani da matakan kariyar cutar Corona.

Yayin wata bita da a ka shiryawa jami’an hukumar kula da makarantun Alkur’ani da Islamiyya tajihar Kano a kan kare kai daga cutar Covid-19 wanda gidauniyar Khalifa Dankade ta hada tare da hadin gwiwa da hukumar da kuma cibiyar bincike a kan cututtuka ma su yaduwa ta jami’ar Bayero.

Ya ce”Hakan ne zai iya yakar cutar yadda ya kamata”

A nasa bangaren shugaban hukumar makarantun Alkur’ani da na Islamiyyu na jihar Kano, Goni Yahuza Dan Zarga cewa ya yi”Bitar abu ne mai amfani, kuma za mu yi amfani da wannan damar”.

Shugaban gidauniyar ta KDC, Khalifa Mustapha Dan Kade cewa ya yi”Bitar mun yi ta ne domin wayar da jami’an mu yadda za su kare kan su daga cutar”.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa Malaman tsangayu daga kananan hukumomi daban-daban ne a Kano su ka halarci taron bitar.

Continue Reading

Labarai

Bature ya fara biyan makudan miliyoyi sakamakon asarar sassan jikin wani mai gadi

Published

on

Wata babbar kotun jihar Kano mai lamba 11 dake zaman ta a Mila Road karkashin mai shari’a R.A Sadiq ta yi umarnin wani bature ya biya wani matashi Naira miliyan goma sha uku da dubu dari daya. Sakamakon kade matashin da wani bature mai aiki a kamfanin Gongoni ya yi da mota a rukunin masana’antu a yankin Sharad har kuma matashin ya rasa ido daya da kafa daya tun a shekarar 2015.

Kotun ta yi umarni a biya matashin kudin cikin watanni bakwai da su ka gabata.

A Talatar nan dai baturen ta hannun lauyan sa sun mika cakin kudi na Naira miliyan biyar da dubu dari daya ga lauyan da ya tsayawa matashin wato Abdul Adamu Fagge, Inda za su cigaba da biyan naira miliyan biyu duk wata za kuma su fara biya daga watan gobe, wato watan Agusta kamar yadda wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito.

Haka zalika tun a lokacin kuma batun yake a kotu inda daya daga cikin lauyoyin ma su zaman kan su a jihar Kano, Abdul Adamu Fagge ya tsayawa matashin kyuata har kuma a ka sami nasara.

 

 

Continue Reading

Manyan Labarai

Alonso zai koma wasan tseren Mota

Published

on

Mai rike da kambun gasar tseren mota na Formula One har sau biyu, Fernando Alonso zai dawo gasar tseren mota a sabuwar shekara mai kamawa.

Fernando Alonso wanda zai cika shekaru 39 a wanan watan ya rattaba yarjejeniya da kamfanin mota na Renault wanda ya nuna cewa zai ci gaba da yin wasan tseren mota.

A shekarar 2018 ne Alonso ya bar gasar tseren mota lokacin da ya yi  kokarin lashe gasar wanda a  ka gudanar a Indianapolis a watan Agusta da motar sa ta McLaren.

Alonso zai kasance da dan kasar Faran sa Esteban Ocon wanda zai sauya dan kasar Australiya Daniel Ricciardo.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish