Connect with us

Manyan Labarai

Rashin takardun gwajin jinin Ango ya janyo amfasa daurin aure a Kano

Published

on

Al’amarin dai ya faru ne a kauyen Bundum mazabar wangara dake karamar hukumar Tofa a jihar Kano, bayan an gabatar da takardar gwajin jinin Amarya wadda ta tabbatar da lafiyar ta, sai limamin daurin auren, Muhammad Lawan ya tambayi cikakkun takardun shedar gwajin jinin Ango waliyan sa suka ce babu, shi kuma limamin, ya ce ba zai daura auren ba har sai inda takardun.

Jin wannan batun ne shima waliyin Amarya mai suna Sani Inuwa da sauran madaura auren suka goyi bayan lallai sai an kawo takardun gwajin jinni na Angon sannan za a daura auren.

Wannan al’amarin dai ya matukar tada hankalin waliyan Ango Kabiru Ibrahim, nan take ya tuntubi Angon Abdurrashid Shehu, nan take ya ce” Ya yi gwajin jinin amma takardar sakamakon ne aka manta ba’a tafi da ita ba wurin daurin auren”. A cewar Ango.

Wannan ya sanya ba a daura auren ba a lokacin har sai da aka jira a akaje aka dauko takardun, aka kuma tabbatar ta lafiyar Angon ce sannan aka daura auren.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki, ya rawaito cewa cikin  ‘yan kwanakin nan a yankin na Tofa, sau biyu aka fasa daurin aure kwata-kwata, bayan an riga an taru, na farko sabida takardar gwajin jini ta nuna cewar Amaryar na dauke da juna biyu, karo na biyun kuma takardar gwajin jinin ta nuna cewar Angon na dauke da cuta me karya garkuwar jiki wato (HIV).

Labarai

An yi wa jami’an hukumar makarantun Alkur’ani da Islamiyya bita a kan Corona

Published

on

Shugaban cibiyar bincike kan cututtuka ma su yaduwa ta jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Isah Sadiq Abubakar ya bukaci al’umma su ci gaba da amfani da matakan kariyar cutar Corona.

Yayin wata bita da a ka shiryawa jami’an hukumar kula da makarantun Alkur’ani da Islamiyya tajihar Kano a kan kare kai daga cutar Covid-19 wanda gidauniyar Khalifa Dankade ta hada tare da hadin gwiwa da hukumar da kuma cibiyar bincike a kan cututtuka ma su yaduwa ta jami’ar Bayero.

Ya ce”Hakan ne zai iya yakar cutar yadda ya kamata”

A nasa bangaren shugaban hukumar makarantun Alkur’ani da na Islamiyyu na jihar Kano, Goni Yahuza Dan Zarga cewa ya yi”Bitar abu ne mai amfani, kuma za mu yi amfani da wannan damar”.

Shugaban gidauniyar ta KDC, Khalifa Mustapha Dan Kade cewa ya yi”Bitar mun yi ta ne domin wayar da jami’an mu yadda za su kare kan su daga cutar”.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa Malaman tsangayu daga kananan hukumomi daban-daban ne a Kano su ka halarci taron bitar.

Continue Reading

Labarai

Bature ya fara biyan makudan miliyoyi sakamakon asarar sassan jikin wani mai gadi

Published

on

Wata babbar kotun jihar Kano mai lamba 11 dake zaman ta a Mila Road karkashin mai shari’a R.A Sadiq ta yi umarnin wani bature ya biya wani matashi Naira miliyan goma sha uku da dubu dari daya. Sakamakon kade matashin da wani bature mai aiki a kamfanin Gongoni ya yi da mota a rukunin masana’antu a yankin Sharad har kuma matashin ya rasa ido daya da kafa daya tun a shekarar 2015.

Kotun ta yi umarni a biya matashin kudin cikin watanni bakwai da su ka gabata.

A Talatar nan dai baturen ta hannun lauyan sa sun mika cakin kudi na Naira miliyan biyar da dubu dari daya ga lauyan da ya tsayawa matashin wato Abdul Adamu Fagge, Inda za su cigaba da biyan naira miliyan biyu duk wata za kuma su fara biya daga watan gobe, wato watan Agusta kamar yadda wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito.

Haka zalika tun a lokacin kuma batun yake a kotu inda daya daga cikin lauyoyin ma su zaman kan su a jihar Kano, Abdul Adamu Fagge ya tsayawa matashin kyuata har kuma a ka sami nasara.

 

 

Continue Reading

Manyan Labarai

Alonso zai koma wasan tseren Mota

Published

on

Mai rike da kambun gasar tseren mota na Formula One har sau biyu, Fernando Alonso zai dawo gasar tseren mota a sabuwar shekara mai kamawa.

Fernando Alonso wanda zai cika shekaru 39 a wanan watan ya rattaba yarjejeniya da kamfanin mota na Renault wanda ya nuna cewa zai ci gaba da yin wasan tseren mota.

A shekarar 2018 ne Alonso ya bar gasar tseren mota lokacin da ya yi  kokarin lashe gasar wanda a  ka gudanar a Indianapolis a watan Agusta da motar sa ta McLaren.

Alonso zai kasance da dan kasar Faran sa Esteban Ocon wanda zai sauya dan kasar Australiya Daniel Ricciardo.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish