Connect with us

Manyan Labarai

Akwai dokokin kawo ziyara gidan ajiya da gyaran hali –DSC Misbahu

Published

on

Mai magana da yawun hukumar gidajen ajiya da gyaran tarbiya na jihar Kano, DSC Misbahu Kofar Nasarawa ya ce, ba ka ra zu be ake kai ziyara gidan ajiya da gyaran hali ba, akwai dokoki da kuma ranakun kai ziyarar.

DSC Misbahu ya bayyana hakan ne a zantawar su da gidan rediyon Dala ta cikin shirin Shari’a a Aikace na gidan rediyon Dala.

Ya na mai cewar, “Mu kan ware ranakun ziyara, akan yi Litinin, Talata, Laraba, Alhamis da kuma Lahadi, amma ana dauke ranakun Juma’a da Asabar, idan za ka kai ziyarar dan uwanka ya na ciki za ka je da safe misalin karfe Tara, a dauki sunanka a rubuta da lambar waya, a tambayi menene dangantakarka da wanda ya ke cikin gidan, sannan a shiga da kai ka gana da dan uwanka.”

Ga wanda bai sani ba, me ne ne ba a son shiga da shi domin kaucewa taka doka?

“Abubuwan da ba a son a shiga da su kusan dukkan abubuwan da mu ka sani ne, kamar akwai kwayoyi wanda kowa ya san sun sabawa doka, kuma ko maigida ba zai so a shigar ma sa da kwaya ko wiwi cikin gida ba, duk wani nau’inkan kayan laifuka da dokar kasa ta hana mu ma ba zamu so a shigar mana da su ba.”  Inji DSC Misbahu

Ya kuma kara da cewar, idan suka kama mutum ya karya doka sun a mika shi bangaren da ya dace, wurin ‘yan sanda ko hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, sannan ya yi kira da al’umma da su bi dokar gidan su zauna lafiya.

 

 

 

Manyan Labarai

Fadan dabar kofar Na’isa da kofar Dan-agundi, laifin iyaye – Mazaunin Yankin

Published

on

Wani mazaunin ƙofar Na’isa wanda ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce faɗan dabar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin da Ɗan Agundi, laifin iyaye ne, da kuma wasu manya a unguwannin da ake zargin suna goya musu baya ta hanyar daƙile yunƙurin hukumomi na ɗaukar doka a kansu.

Mutumin ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, biyo bayan yadda rikicin faɗan dabar ya sake ɓarkewa a unguwannin a Alhamis ɗin nan, al’amarin da ya janyo asarar dukiyoyin al’umma a yankunan.

Ya ce lamarin ya faro ne tun a lokacin bikin ƙaramar Sallah, lamarin da a baya ƙura ta lafa, sai dai kuma a ranar Alhamis ɗin sai gashi an sake samun faɗan dabar.

A cewar sa, “A lokacin faɗan dabar ya faru an Sassari mutane da dama, hatta Saniya ma ba ta tsira ba sai da aka sareta, tare da fasa gilasan ababen hawan Mutane, “in ji shi”.

Sa dai mutumin ya ce, tuni jami’an tsaron Ƴan Sanda, suka kai ɗauki tare da kwantar da tarzoma, lamarin da ƙurar ta lafa.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ba za mu amince da yadda ake yawan kai wa jami’an mu hari ba a Kano – KAROTA

Published

on

Hukumar kula da zirgar-zirgar ababen Hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta ce ba za ta lamunta da yadda ake yawan kai wa jami’anta farmaki ba, na ba gaira babu dalili yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Shugaban Hukumar KAROTA, a Kano, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya yi wannan gargaɗin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 09 ga watan Afrilun 2025.

“Hakan na zuwa ne biyo bayan wani mummunan hari da wasu mutane da ke cikin baburin Adai-daita sahu suka kai wa jami’an na mu yayin da suke tsaka da aikinsu a titin da ke dab da gidan Buhari kan hanyar zuwa Gidan Zoo, “in ji shi“.

Sanarwar ta ce, tunda farko an tsayar da wani mai baburin Adai-daita Sahu ne inda yaƙi tsayawa, sai kawai aka hango mai ɗan sahun ya naushi jami’in karotar.

Sai dai a ta bakin Shugaban kungiyar ‘Yan Adai-daita Sahu a jihar Kano, ya ce waɗannan mutane ba halattattun ‘Yan Adai-daita Sahu ba ne, sun dai fake da sana’ar su dan aikata ta’addanci.

Daga bisani dai jami’n hulɗa da jama’a na Hukumar Koratar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya ce hukumar za ta ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, don kare afkuwar irin hakan a gaba.

Hukumar ta ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ya shafe ta, ko kuma ƙorafe-ƙorafe, zai iya kiran waɗannan lambobin domin sanar da ita, da suka haɗar da 09015709449 ko 08059689422 ko kuma 08067311520.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Continue Reading

Trending