Connect with us

Labarai

Zamu wayar da kan ma’aikatan mu sakamakon bular sabuwar cuta- AKTH

Published

on

Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, ya ce zai gudanar da kwarya-kwaryar bita ga dukannin ma’aikatan sa yadda za su gudanar da ayyukan su sakamakon zargin bullar wata bakuwar cuta mai suna Pyrexia.

sanarwar mai kunshe da sa hannun, Dr Auwal Umar Gajida , ta ce a safiyar gobe Laraba kafatanin jami’an asibitin za su hallara domin wayar da kan su kan bullar bakuwar cutar.

sanarwar ta kuma shawarci dukkanin ma’aikatan ta cewa da su nutsu tare da sanya ido da kuma bada kulawa yayin da suke aiwatar da ayyukan su a kan marasa lafiya.

Yanzu haka dai mahukunta a asbitin na AKTHA tare da ma’aikatar lafiya ta Nijeriya na gudandar da bincike a kan cutar.
An kuma bukaci ma’aikatan asibitin su kaucewa bayyana ra’ayin su kan lamarin a shafukan sada zumunta, gudun kada hakan ya haifar da tsoro a zukatan al’umma.

Yanzu haka dai asibitin an tabbatar da mutuwar wasu likitoci biyu a asibitin wadanda ake zargin cutar ce ta shafe su yayin da aka kuma killace mutum guda domin kulawa da lafiyar sa.

Labarai

Matashin da ke Sansana bayan Akuya yana sakawa a TikTok ya shiga hannun hukumar Hisbah a Kano

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani Matashi da aka yi zargin ya sansana bayan wata Akuya, a matsayin yana son ya yi suna a shafukan sada zumunta.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah Dakta Mujahideen Aminudeen Abubakar, ya shaidawa Dala FM Kano cewar, sun kama matashin ne mai suna Shamsu Yakubu dan garin Dawakin kudu, mai shekaru 24, bayan da dagacin garinsu ya kawo korafi akansa.

Dagacin ya ce an kai ƙorafin matashin ne saboda yadda mutanen garin suka yi kokarin farmasa, bayan da aka gano bidiyonsa a shafin TikTok yana sansana bayan Akuya.

Yanzu haka hukumar ta ɗauki matakin kai matashin a fara yi masa gwajin Ƙwaƙwalwa, da kuma na ta’ammali da kayan maye.

Continue Reading

Labarai

Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.

Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.

Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.

A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

Continue Reading

Labarai

Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.

Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.

“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.

Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.

Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

Continue Reading

Trending