Connect with us

Labarai

Kafa kungiyoyin al’umma zai magance matsalar tsaro.

Published

on

Shugaban karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano’ Kabiru Ado Fanshekara, ya ce samar da kungiyoyi a cikin al’umma ya na kawo gagarumar cigaba da samun nasara a tsakanin matasa.

Kabiru Ado Fanshekara,ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakin sa, Sagir Abdullahi Fanshekara, a yayin kaddamar da kungiyar cigaban karamar hukumar Kumbotso, mai suna Kumbotso Progressive Forum (KPF) wanda aka kaddamar a karshen makon da ya gabata.

Ya kuma ce”Matukar a ka samu yawaitar kungiyoyin kishin al’umma musamman ma a cikin unguwanni, hakan zai kawo cigaba mai tarin yawa a tsakanin jama’a”.

Shima a nasa jawabin shugaban kungiyar ya ce” Dalilin da ya sanya muka bude kungiyar munyi domin mu tallafawa al’ummar Kumbotso wajen abun da suka shafi harkokin tsaro da ilimi da zamantakewa tare da ganin mun hada kai da dukannin masu daura damara a yankunan mu sun bada gudunmawar su a harkokin tsaro”. Inji Maikudi Musa.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar, ya rawaito cewa al’umma da dama ne suka halarci taron cikin su kuwa har da hakimin Kumbotso da sauran masu rike da masarautun gargajiya na yankin.

Labarai

Abin takaici ne yadda ake fuskantar ƙarancin ruwan Sha a sassan jahar mu – Gwamnan Kano.

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya nuna rashin jin daɗin sa bisa yadda ake samun ƙarancin Ruwan Sha, a wasu daga cikin sassa jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, a lokacin a ya kai ziyarar gani da ido, matatar Ruwa da ke Tamburawa a yammacin yau Juma’a, a ƙokarin sa na na gyara ɓangaren ruwan a cikin garin Kano.

Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma sha alwashin tabbatar wa al’umma cewar, gwamnatin sa za ta yi aiki ba dare ba rana domin tabbatar da isasshen ruwan Sha ga al’ummar jihar Kano.

Gwamnan ya ƙara da ce a lokacin da suka zo ba sufi mako biyu ba suka samar da ingantaccen Ruwan sha, wanda ya rinƙa shiga cikin lunguna da Sako na sassan jihar.

Continue Reading

Labarai

Ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da sayar da Burtalai a wasu garuruwan ta

Published

on

Biyo bayan kokawar da wasu Fulani Makiyaya suka yi kan yadda wasu suka gididdiba burtalai yayin da aka siyarwa Manoma, a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, yanzu haka ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da taɓawa, ko kuma sayar da dukkanin Burtalan kiwon shanun ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban riƙon ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu a kan taɓa dukkan guraren, a dan haka sun dakatar da dukkanin yunƙurin taɓa Burtalan har sai shugabanni na kwamitin ƙasa sun kammala bincike wanda yanzu haka ake ci gaba da yi.

Da yake nuna jin daɗin sa kan matakin dakatarwar, amadadin Fulanin garuruwan, shugaban ƙingiyar Funali Makiyaya ta Gan Allah, Ahmad Shehu Gajida, yabawa gwamnatin jihar Kano, da kuma ƙaramar hukumar ta Tofa ya yi, bisa karɓar koken su da suka akai.

A baya-bayan nan ne dai a zantawar Dala FM Kano, da wasu Funalani Makiyaya mazauna garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, suka koka kan yadda aka gididdiba burtalan a yankunan nasu aka siyarwa manema, lamarin da suka ce ka iya sawa su rasa guraren da za suyi kiwon shanun su wanda hakan babbar barazana ce a gare su.

Continue Reading

Labarai

Ku guji zubar da Shara barkatai a muhallan ku – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi al’umma da su kaucewa zubar da shara a wuraren da ba’a tanade su ba, domin kaucewa yawaitar samun cutuka a tsakanin al’umma, duba da yadda ake ci gaba da tunkarar lokacin Damuna.

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambasada Ahmadu Haruna Zago, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake sanya ido kan aikin kwashe sharar da ke unguwar Zango hauran gadagi bayan Festival.

Ya ce duba da yadda Damuna ke ci gaba da tunkarowa, akwai bukatar al’umma su fahimci cewa zubar da shara barkatai ka iya haifar da cututtuka daban-daban ga iyalan su, musamman ma kasancewar sharar da ke unguwar ta Zango bayan Festival, tana tsakiyar gidajen al’umma ne da kasuwa da kuma makaranta.

Nazifi Mohammed Usman mai Duniya, da Mohammed Ibrahim wato Halifa mai Gas mazauna unguwar ta Zango ne, sun ce tarin sharar a cikin unguwar su babban ƙalubale ne a gare su, domin kuwa taruwar da tayi har ta kan shiga cikin makarantar yankin su.

Shugaban hukumar kwashe sharar Ahmadu Zago, ya kuma sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen tsafta ce birnin Kano, wajen kwashe shara daga kowane yankin, domin gudun faruwar ambaliyar ruwa sanadin sharar da ka toshe magunan ruwa a jihar Kano.

Continue Reading

Trending