Connect with us

Labarai

Tsaftar Muhalli na magance zazzabin Lassa- Dr Hadiza Galadanchi

Published

on

Kwararriyar likita a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano (AKTH), Farfesa Hadiza Galadanci, ta ja hankalin al’umma da su kara himmatuwa wajen kulawa da tsaftace muhallin su domin kare kai daga kamuwa da cututtuka, musamman ma cutar zazzabin Lassa.

Farfesa Hadiza Galadanci, ta na wannan jawabin ne a yayin da kungiyar matasan likitoci masu tasowa dama masu koyon aikin likita na unguwar filin Mushe dake karamar hukumar Gwale, Suka shirya taron tallafawa al’umma da gwajin lafiya da kuma basu magani kyauta a karamin asibitin filin Mushe, a karshen makon da ya gabata.

Ta ce,”Tsaftace muhalli zai taimaka wajen samarda ingantacciyar lafiya tare da kare kai da kamuwa da cutuka masu yaduwa musamman wadanda a ke samun su a cikin gida”.

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar matasan likitocin, Sanata Khalid Sunusi Kani ya ce” ni kirana da zan yi shi ne, sauran kungiyoyin cikin al’umma da su rinka tallafawa al’ummar su musamman ma marasa karfi a bangaren lafiya da ma sauran abubuwan da suka shafi al’umma marasa karfi”. Inji Kani

Suma wasu daga cikin wadanda su ka amfana da tallafin sun nuna godiyar su ga kungiyar sakamakon duba su da suka yi tare da basu magani kyauta.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, ya rawaito cewa, fiye da mutane dari uku (300) ne suka amfana wadan da suka hadar da maza da mata.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending