Connect with us

Labarai

Likitan bogi ya shiga hannun hukuma

Published

on

Hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu karkashin kulawar gwamnatin jihar kano tare da hadin gwiwar kungiyar likitoci ta kasa NMA ta kama wani likitan bogi mai suna Ibrahim Adamu wanda ya shafe tsawon shekaru ya na aikin lafiya a matsayin kwararran likita a wani asibitin Kano da ma wasu jihohin.

Jim kadan bayan holin likitan bogin ga manema labarai da sakataran zartaswar na hukumar, Dr Usman Tijjani Aliyu, ya yi jawabin sa inda ya ce” mun jima muna bibiyar likitan bogin tsawon lokaci amma bamu samu nasarar kama shi ba kasancewar ba shi da tsayayen asibitin da ya ke zama”.

Ya kuma ce” Yanzu haka likitan da ake zargi na bogin ya na chaji ofis din yansanda a tsare, kuma tuni ya yi ma na bayanin takardun da yake amfani dasu na aiki inda ya tabbatar mana cewa na wani mutum ne da yake da gogewa a fanin lafiya kuma yake neman aikin bai samu ba”.

Ya kuma kara da cewa” Ko a shekarar 2014 an taba kama shi aka kuma gurfanar da shi a gaban kotun majistre dake Koki, kuma mun sha alwashin wannan karin zamu kara gurfanar da shi har sai mun ga an tabbatar da hukuncin da zai sa ba zai kara yin sojan gona ba”.

A cikin wata takarda mai kunshe da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar lafiya ta jihar Kano, Isma’il Garba Gwammaja ya sanyawa hannu, ta rawaito cewa, Dakta Usman Tijjani Aliyu ya kuma gargadi al’umma da su za ma masu taka tsan-tsan tare da sanar da hukuma mafi kusa dasu domin daukar matakin gaggawa ga duk wani likitan da basu gamsu da aikin sa ba.

Labarai

Mahukunta ku kawo mana ɗauki a masallacin garin mu – Mazauna garin Ɗan-Dalama

Published

on

Al’ummar garin Ɗan-Dalama da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta kan yadda katangar masallacin Juma’a na garin ta lalace, lamarin da hakan ke barazanar faɗuwar katangar.

Shugaban kwamitin masallacin juma’ar na garin Ɗan Dalama, Mallam Muhammad Mai Nama, ne ya magantu kan al’amarin, inda ya kuma yi kira ga al’umma ciki har da Attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, da su kawo musu ɗauki domin gyara katangar masallacin na Ɗan Dalama, bisa yadda take neman faɗuwa.

Ya kuma ƙara da cewa ba iya katangar ce ke barazanar faɗuwar ba, haka ma cikin masallacin ba a cewa komai, duk kuwa da ƴan kwamitin sun yi bakin ƙokarin su, amma dai kawo yanzu akwai gyare-gyaren da ya ke buƙata.

Continue Reading

Labarai

Ba za’a iya wadata mutane da Fetur ba idan gwamnati ba ta sa hannu ba – Bashir Ɗan Mallam

Published

on

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar man fetur a ƙasar nan, shugaban kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas, ta ƙasa Bashir Ahmad Ɗan malam, ya ce koda kuwa matatar Mai ta Dangote za ta yi ƙarfi ka’in da na’in, ba lallai ne a samu saukin Man fetur ba a ƙasa, matuƙar gwamnatin tarayya bata sa hannu ba.

Bashir Ɗan Malam ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar yau Juma’ar.

Ɗan Mallam ya kuma ce sakamakon yadda gwamnati take taimakawa a fagen shan man, hakan yasa idan har bata sanya hannu ba za’a rinƙa shan wahala wajen samun man fetur ɗin a ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar man fetur, lamarin da ya sa ake siyar da kowacce lita sama da Naira 800 a jihar Kano, inda ake ci gaba da fuskantar manyan layuka a gidajen man da dama.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.

Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.

Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.

Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.

Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.

Continue Reading

Trending