Labarai
Al’ummar Danbare sun koka kan rashin ofishin ‘yan sanda
Mai unguwar Danbare (D) dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, Saifullahi Abba Labaran, ya ce yanzu haka sun shawo tarin matsalolin da unguwar Danbare ke fuskanta a yankin baki daya.
Saifullahi Abba Labaran, na wannan jawabin ne a ganawarsa da gidan rediyon Dala.
Ya ce” Yanzu sace-sace a unguwar mu ta Danbare an magance ta domin kuwa yanzu haka za ka iya yin kiwon dabobin ka ba tare da wani fargaba ba, kuma ‘yan sintirin yankina babu dare babu rana komai sanyi suna gudanar da tsaro a yankin baki daya, batun ka ce ka na tsoron yankin yanzu an wucce wurin”.
“Kuma duk wata badala da ake yi a yankin mu yanzu babu wannan maganar mun magance ta saoba duk wanda zai zauna a yankin sai an dauki hoton sa da wurin da yake aiki sannan zamu bashi gida ya zauna. Duk matasalar da muke fama da ita an magance ta, kungiyar gyara kayan ka ta Kumbotso da ta sintiri duk sun shigo cikin lamarin namu, kuma Baturan dansanda na Dorayi Babba ya taimaka mana sosai bias hadin kai da yake bamu”.
“Kuma matasan mu ba daga nan ba saboda kowa ya na da abun yi babu mai zaman kasha wando, kira na ga al’umma da su taya mu da addu’a domin samun zaman lafiya, kuma gwamnati da mahukunta domin a kawo mana ofishin ‘yansanda a yankin saboda in ka duba tun daga Kabuga har kaje Janguza kusan babu unguwa mai girman dan bare”. A cewar mai unguwar Danbare Saifullahi.
Labarai
Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu
Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.
Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.
Labarai
Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya
Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.
A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.
Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.
Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.
Labarai
Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano
Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.
Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.
Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.
A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.
Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su