Connect with us

Lafiya

Tallafi ya isa wurin da ibtila’in rusau ya shafa

Published

on

Mutane 120 ne daga cikin wadanda iftila’in ambaliyar ruwa da gobara suka shafa a karamar hukumar Nasarawa, suka amfana da tallafin buhunan siminti biyar da kwanon rufi bandir daya kowanen su.

Jim kadan bayan kammala mika kayayyakin, yau a shelkwatar karamar hukumar, shugaban karamar hukumar Nassarawa, Lamin Sani ya bukaci wadanda suka amfana da tallafin da su yi kyakkawan amfani da shi wajen mayar da gine-ginen na su da suka rushe tun a baya.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun ce dama ai sun dade suna ta kokarin ganin wannan ranar tun tuni daga wurin gwamnati amma basu samu ba sai a wannan lokacin.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki, ya rawaito cewa tallafin shi ne irin sa na biyu da karamar hukumar ta gabatar a kwana-kwanan nan wanda kuma nan bada jimawaba a ke sa ran za a gabatar da karo na uku.

Labarai

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta sassauta lockdown a Kano

Published

on

Shugaban kwamitin kar ta kwana kan cutar Covid-19 na gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya tabbatar da cewa za a ci gaba da rufe makarantu har nan da wasu lokutan daga karfe 6 na safe zuwa karfe 8 na dare.
A zaman kwamitin na yau a birnin tarayyar Abuja Boss Mustapha ya sanar da hakan, cewa yanzu haka an sassauta dokar kullen a jihar Kano sannan za a bude ofisoshin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi ma su matakin aiki 14 zuwa sama za su rinka zuwa aiki tun daga karfe 9 na safe har zuwa karfe 2 na ranakun Litinin zuwa Juma’a.
Haka zalika a yayin sanarwar ta ce za a ci gaba da rufe iyakokin jihohi, sai dai kawai banda ma su motocin kayayyakin abinci da makamantan su.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish