Connect with us

Lafiya

Wasu daga hudubobin juma’a a Kano

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Abdullahi Ibn Mas’ud dake unguwar Kabuga ‘yan Azara, Malam Zakariyya Abubakar ya bukaci mutane da su tashi tsaye wajen umarni da kyakkawan aiki da kuma hani da mummuna ta yadda al’ummar baki daya za ta samu tsira daga faruwar musifu da Annoba.

Malam Zakariyya Abubakar ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar Juma’a daya gabatar yau a masallacin.

Ya kuma ce, “Hani da mummunan aiki da kuma umarni da kyakkawa, ibada ce wadda kowa zai iya yi gwargwadon ikon sa, musamman ma a wannan lokaci da ake samun yaduwar munanan ayyuka a tsakanin al’umma.”

Ya kara da cewa, “Ana gudanar da umarnin da kyakkawan da kuma hani da mummunan ta cikin sauki da nasiha, bawai da cin zarafi ko wulakanci ba.” Inji Malam Zakariya.

Limamin masallacin Juma’ar na Abdullahi Ibn Mas’ud, Malam Zakariyya Abubakar, ya kuma shawarci musulmi da su kasance masu jin tsoron Allah a cikin dukkanin al’amuransu.

 

Shi kuwa limamin masallacin juma’a na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi dake garin Mariri a karamar hukumar Kumbotso, Malam Sunusi Adamu Birnin Kudu, ya ja hanakalin mawadata da su yi kyakkawan amfani da arzikin da Allah ya ba su wajen taimakawa mabukata domin samun guzuri zuwa lahira.

Malam Sunusi ya bayyana hakan ne a hudubarsa da ya gudanar yau juma’a a masallacin.

Ya na mai cewa, “Taimako tsakanin mawadata da masu karamin karfi, ya na taimakawa matuka wajen samar da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin al’umma, dama kuma tunkude faruwar musifu daga dukiyar.”  A cewar Malam Birnin Kudu.

Daga karshe limamin ya kuma gargadi ‘ya’ya dangane da wajabcin yiwa iyayensu biyayya domin da cewa a duniya da kuma ranar gobe kiyama.

A nasa hudubar limamin masallacin juma’a na Umar Sa’id Tudun Wada dake gidan rediyo a yankin unguwar Tukuntawa a karamar hukumar birnin Kano, Gwani Fasihu Muhammad Dan Birni, ya yi kira ga wanzamai da su rinka sa ni tare da neman ilimi a kan bangaren yin shayi ga ‘ya’ya mata da suke yi wa wasu daga cikin su.

Gwani Fasihu Muhammad Dan Birni, ya yi wannan kiran ne a lokacin hudubar sallar juma’a na yau wanda ya gudana a masallacin.

Ya ce” wanzamai da su rinka zuwa neman sa ni kan yadda a ke gudanar da shayi ga ‘ya’ya mata maimakon su rinka yin ta kai tsaye domin hakan na illata ‘ya’ya mata musamman.

Labarai

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta sassauta lockdown a Kano

Published

on

Shugaban kwamitin kar ta kwana kan cutar Covid-19 na gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya tabbatar da cewa za a ci gaba da rufe makarantu har nan da wasu lokutan daga karfe 6 na safe zuwa karfe 8 na dare.
A zaman kwamitin na yau a birnin tarayyar Abuja Boss Mustapha ya sanar da hakan, cewa yanzu haka an sassauta dokar kullen a jihar Kano sannan za a bude ofisoshin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi ma su matakin aiki 14 zuwa sama za su rinka zuwa aiki tun daga karfe 9 na safe har zuwa karfe 2 na ranakun Litinin zuwa Juma’a.
Haka zalika a yayin sanarwar ta ce za a ci gaba da rufe iyakokin jihohi, sai dai kawai banda ma su motocin kayayyakin abinci da makamantan su.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish