Connect with us

Manyan Labarai

Kano: Wani mawaki ya gurfana a kotu

Published

on

Kotun majistret mai lamba 72 karkashin mai Sharia Aminu Gabari ta sanya wani matashi mai suna Buhari Muhammad Kosan waka a hannun beli.

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ce ta gurfanar da Kosai bisa tuhumar bata suna, yunkurin tayar da hankalin al’umma da kuma rera wata waka mai suna a Wanki Gara wadda bata samu sahalewar hukumar ba.

Buhari Kosan waka, mazaunin jihar katsina ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.

Mai Sharia Aminu Gabari ya bayar da belinsa bisa sharadin cewar, sai ‘yan majalisar Dokoki biyu ko Daraktoci biyu daga bangaren Shari’a ko bangaren zartaswa sun tsaya masa.

An kuma ayyana cewar, masu karbar belin sai sun gabatar da takardun shaidar biyan haraji na shekaru 3 sannan idan Kosan ya tsere, masu karbar belinsa za su biya Naira Dubu Dari Biyar.

Labarai

#SecureNorth: Mun gaji da salon mulkin Buhari – ‘Yan Najeriya

Published

on

Ƴan Najeriya sun fara kosawa da salon mulkin gwamnatin kasar da suka ce ta yi biris da sha’anin tsaro.

Wannan na zuwa ne yayinda al’amauran tsaro a arewacin kasar ke kara tabarbarewa, a dai-dai lokacin da alhinin mutuwar manoma 43 da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka yi musu yankan rago a jihar Borno.

Al’ummar kasar dai na ganin munin matalsar tsaro na kara ci musu tuwo a kwarya, lamarin da ya sanya da dama daga cikin al’ummar kasar suka fusata, inda suke bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta.

Abinda kuma ke yawo a kafafenn sada zumunta baya ga batun sai Buharin ya sauka daga mulkin kasar, shine batun a sallami hafsoshin tsaro, akan abinda ‘yan Najeriya ke cewa sun gaza magance matsalar tsaro da ke kara kamari musamman, a arewacin kasar.

Haka zalika al’ummar Najeriya sun ce shugaban ya gaza cika musu alkawuran da ya dauka a lokacin da yake neman kujerar shugabancin kasar, a yayinda tsadar rayuwa ke ci musu tuwo a kwarya.

Yanzu haka dai hankulan mazauna arewa maso yamma da ke fama da matsalar fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a tashe yake, yayinda mazauna yankin arewa maso gabashin kasar ke cikin tashin hankali.

Tun bayan yankan ragon da aka yiwa manoma a kauyen Zabarmari na jihar Borno ne, hankulan jama’a ya kara karkata, yayinda ake ganin mazauna arewacin kasar na cikin tashin hankali, sakamakon tabarbarewar tsaro.

Rundunar sojin Najeriya ta ce har yanzu ana neman wasu daga cikin mutanen da harin ya rutsa da su, yayin da wasu ƴan ƙasar ke ganin ko shugaba Muhammadu Buhari ya tashi tsaye wajen magance matsalar tsaron ko kuma ya sauka daga mulki.

Me ke faruwa a Arewa maso Yamma?

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce manoma 110 ne aka kashe a Zabarmari na jihar Borno, ba 43 ba kamar yadda hukumomin tsaron kasar suka ce.

Majalisar ta bayyana wannan harin a matsayin abu mafi muni da aka yiwa fararen hula, cikin shekarar 2020 a duniya.

A dai-dai lokacin da ake zaman makokin mutuwar manoman ne, kuma rikici ya balle a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, inda rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutum bakwai, sai kananan yara da suka tsere bayan da wasu na daban suka jikkata.

Bayan kwana guda da barkewar rikicin ne, wasu ‘yan bindiga suka tare hanyar Zaria zuwa garin Kaduna, inda suka jikkata mutane, ko da yake kawo yanzu ba a tabbatar da mutuwar ko da mutum guda ba.

Continue Reading

Labarai

Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan kisan manoma a Borno

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta nanata cewa manoma 43 aka kashe, ba 110 da Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe.

Mai Magana da yawun rundunar, John Enenche a wata hira da ya yi da gidan talibijin na Channels, ya ce har yanzu suna tattara bayanai kan mutanen da harin ya shafa domin tabbatar da adadin wadanda suka mutu.

Sai dai rundunar ta ce abinda yake kara ta’azzara batun matsalar tsaro shine, yadda mazauna yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula ba sa kai rahoto ga sojoji da sauran hukumomin tsaro kan halin da suke ciki.

“Mutane da dama basa kawo mana rahoton abinda ke addabar su kan sha’anin tsaro, kuma ba dole bane ka tilastawa mutane su sanar maka abinda ke faruwa.” In ji shi

Ko da yake John Enenche ya ki bayyana yanda rundunar sojin ke tattara bayanata akan wuraren da fama da yake-yake a arewacin Najeriya.

Continue Reading

Labarai

Sabon rikici ya kashe mutum bakwai a Kaduna

Published

on

AKalla mutane bakwai aka kashe a wani sabon rikici da ya barke a yankin karamar Hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun tabbatar da ewa, al’amarin ya faru ne tsakanin daren ranar Asabar wayewar garin ranar Lahadi.

Wata sanarwa da gwamnatin Kaduna ta fitar, ta ce mutane hudu sun jikkata, inda ake fargabar bacewar yaran guda biyu, bayan da aka kone gidaje hudu a yayin rikicin.

Samuel Aruwan, shine kwamishina lura da harkokin tsaro na jihar, ya ce al’amarin ya yi mafari ne bayan kashe wani makiyayi, mai suna Isiyaka Sa’idu, ranar Asabar a Unguwan Pah da ke karamar Hukumar Jema’a din.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!