Connect with us

Labarai

Ganduje ya fara binciken ciyarwa a makarantun Firamare

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamitin da zai binciki yadda a ke ciyar da daliban firamare a fadin jihar Kano.

Daliban makarantar Firamaren Dan Isaa.

Kwamitin karkashin jagorancin hukumar Hisba, ta fara bibiyar al’amuran ne tun a cikin makon nan wanda ta fara rangadin gudanar da binciken karkashin babban Kwamadan hukumar, Sheikh Muhammad Haruna Ibn Sina.

Daliban sun yi layi a na zuba masu taliya samfurin macaroni kowa rabin ludayi.

Cikin zagayen na ranar Laraba, karkashin mataimakin babban kwamandan hukumar mai kula da bangaren Da’awah, Murtala Muhammad Adam, wanda su ka ziyarci makarantu uku daga yankin karamar hukumar Rimin Gado.

Masu dafa Macaroni mai da yaji suna aikin gaurayawa kafin su rabawa dalibai a Firamaren Butu-Butu.

Cikin makarantu da hukumar ta ziyarta ta fara yada zango ne a Firamaren Butu-Butu, wanda ta tarar da a na kokarin gauraya Taliya samfarin Macaroni da man gyada da yaji, wanda masu dafa abincin suka bayyana cewa su ma a haka a ka umarce su tare da baiwa dalibai dafafiyar Macaroni da mai da yaji kusan leda 7 ga dalibai sama da 350.

Dafa dikar Macaroni da za a rabawa dalibai a Firamaren Dan Isaa.

Haka zalika hukumar bayan daukar adadin dalibai maza da mata a makarantar ta kuma wuce makarantar Firamaren Dan Isa da firamaren Dan Isaar Kanawa a yankin, wanda nan ma hukumar ta Hisba ta duba yadda a ke raba abincin ciki kuwa akwai shinkafa da Macaroni wake da Biskit harma da Dambu a dukannin ranaku biyar. Sai dai a cikin makarantun malaman makarantun Firamaren sun koka kan rashin basu isasun kayan abinci da man girki inda suka bayyana cewa ciki harma kudin su ne yake shiga sakamakon karancin abincin da bay a isar daliban wanda wasu dole sai chokali daidai suke samu wasu kuwa a makarantun rabin ludayin roba suke samu.

Dafa dikar macaroni da a ke rabawa daliban makarantar Dan Isaar Kanawa.

A nasa jawabin, jagoran tafiya a yankin Rimin Gado, Murtala Muhammad Adam, ya bayyana takaicin sa sakamakon yadda suka tsinci a na rabawa daliban abincin.

Dalibai na dakon a raba masu abinci a cikin ajujuwan su.

Malaman makarantun sun bayyana cewa suna ciyar da daliban ne tun daga matakin ajin Firamare na daya har zuwa na hudu a gwamnatin jiha sai kuma matakin ajin firamare na biyar da na shida gwamnatin tarayya ke ciyar da daliban.

Kwamitin CRC shi ne dai mai kula da alhakin ciyar da daliban makarantun firamaren jihar Kano.

 

 

 

Labarai

Mahukunta ku kawo mana ɗauki a masallacin garin mu – Mazauna garin Ɗan-Dalama

Published

on

Al’ummar garin Ɗan-Dalama da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta kan yadda katangar masallacin Juma’a na garin ta lalace, lamarin da hakan ke barazanar faɗuwar katangar.

Shugaban kwamitin masallacin juma’ar na garin Ɗan Dalama, Mallam Muhammad Mai Nama, ne ya magantu kan al’amarin, inda ya kuma yi kira ga al’umma ciki har da Attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, da su kawo musu ɗauki domin gyara katangar masallacin na Ɗan Dalama, bisa yadda take neman faɗuwa.

Ya kuma ƙara da cewa ba iya katangar ce ke barazanar faɗuwar ba, haka ma cikin masallacin ba a cewa komai, duk kuwa da ƴan kwamitin sun yi bakin ƙokarin su, amma dai kawo yanzu akwai gyare-gyaren da ya ke buƙata.

Continue Reading

Labarai

Ba za’a iya wadata mutane da Fetur ba idan gwamnati ba ta sa hannu ba – Bashir Ɗan Mallam

Published

on

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar man fetur a ƙasar nan, shugaban kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas, ta ƙasa Bashir Ahmad Ɗan malam, ya ce koda kuwa matatar Mai ta Dangote za ta yi ƙarfi ka’in da na’in, ba lallai ne a samu saukin Man fetur ba a ƙasa, matuƙar gwamnatin tarayya bata sa hannu ba.

Bashir Ɗan Malam ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar yau Juma’ar.

Ɗan Mallam ya kuma ce sakamakon yadda gwamnati take taimakawa a fagen shan man, hakan yasa idan har bata sanya hannu ba za’a rinƙa shan wahala wajen samun man fetur ɗin a ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar man fetur, lamarin da ya sa ake siyar da kowacce lita sama da Naira 800 a jihar Kano, inda ake ci gaba da fuskantar manyan layuka a gidajen man da dama.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.

Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.

Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.

Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.

Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.

Continue Reading

Trending