Connect with us

Lafiya

COVID -19: Gwamnatin Kano zata yi wa mutanen Kano jawabi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai yi wa al’ummar jihar Kano jawabi kan bullar Annoba cutar Corona da aka samu a kasar nan da ma duniya baki daya a yu Litinin.

Wata sanarwa daga Sakataren yada labaran Gwamnan jihar Kano Abba Anwar ya shaidawa Dala FM, cewar, ana sa ran Gwamnan zai yi jawabin ne da misalin karfe biyu na rana, kuma za a yada shi kai tsaye a gidan rediyo da Talabijin mallakar gwamnatin jihar Kano, da wasu daga cikin gidajen rediyo masu zaman kan su.

Haka kuma gwamnan zai yi bayani kan muhimmancin tsaftace jiki da wanke hannaye kamar yadda masana kiwon lafiya ke bayyanawa.

Kawo yanzu dai mutane 36 ne ake zargin sun kamu da cutar ta COVID- 19 a Najeriya yayin da mutum guda ya rasa ran sa.

 

Labarai

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta sassauta lockdown a Kano

Published

on

Shugaban kwamitin kar ta kwana kan cutar Covid-19 na gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya tabbatar da cewa za a ci gaba da rufe makarantu har nan da wasu lokutan daga karfe 6 na safe zuwa karfe 8 na dare.
A zaman kwamitin na yau a birnin tarayyar Abuja Boss Mustapha ya sanar da hakan, cewa yanzu haka an sassauta dokar kullen a jihar Kano sannan za a bude ofisoshin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi ma su matakin aiki 14 zuwa sama za su rinka zuwa aiki tun daga karfe 9 na safe har zuwa karfe 2 na ranakun Litinin zuwa Juma’a.
Haka zalika a yayin sanarwar ta ce za a ci gaba da rufe iyakokin jihohi, sai dai kawai banda ma su motocin kayayyakin abinci da makamantan su.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish