Connect with us

Labarai

Wata gobara ta kone dukiya mai tarin yawa a Kano

Published

on

Wata gobara da ta tashi a daren jiya Lahadi a yankin Tudun Maliki dake jihar Kano, wadda tayi sanadiyyar barnatar da dukiya mai tarin yawa baya ga kone wasu gidaje biyu.

Wutar wadda rahotannin suka bayyana cewa ta shafe sa’o’i biyu tana ci kafin daga bisani jami’an hukumomin kashe gobara na Gwamnatin Jaha dana Tarayya su samu nasarar Shawo kanta.

Wakilinmu da ya halaci Unguwar ta Tudun Maliki ya zanta da wadanda gobarar da konawa gidajen wanda suka bayyana cewar, wutar ta kone duk wasu kayan amfani, sai dai an samu nasarar fito da yara da matan dake cikin gidajen.

A zantawar wakilin mu Abba Isah Muhammad, da Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Gwamnatin Tarayya reshen Jihar Kano Nura Abdulkadir Mai Gida, ya ce, “     Zuwa yanzu babu wanda ya jikkata yayin gobarar kuma bincike ne zai tabbatar da musabbabin faruwarta”. A cewar Nura Maigida.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewar mazauna yankin na Tudun Maliki Sun bayar da gudunmawa wajen tsayarda wutar daga tsallakawa makotan gidajen yayin da gurin ya kasance bisa kulawar jami’an Yansanda dan tsare rayuka da dukiyar alummar yankin daga bata gari.

Labarai

Mai horas da kungiyar Southampton ya kara rattaba sabon kwantiragi

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Southampton, Ralph Hasenhuttl ya kara rattaba sabon kwantiragi a kungiyar ta Southampton.

Ralph Hasenhuttl mai shekaru 52 dan kasar Austrian ya karbi kungiyar ne tun a watan Disamba na shekarar 2018 wanda ya tsallake da su fadawa zuwa ajin ‘yan dagaji.

Mai horaswar ya dai rattaba sabon kwantiragi na tsawon shekaru hudu wanda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024.

Southampton dai ita ce kungiya da ta taba kwasar kashin ta a hannu har tsawon kwallaye tara da a ka zura mata a raga a gasar wanda Leicester City ta lallasa ta.

Continue Reading

Labarai

Naji dadi matuka da za a dawo gasar Premier -Mai horas da Liverpool

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce ya ji dadi sakamakon dawowa da za a yi gasar Firimiya a ranar 17 ga watan Yunin nan.

Klopp ya tabbatar da hakan ne ayayin tattaunawar sa da gidan rediyon BBC ya na mai cewa ya yi kewar wasan sakamakon hutun da a ka tafi na dakatar da wasan a ranar 13 ga watan Maris.

Ya ce” Na yi rashi sosai wannan abun mamaki ne domin kuwa abu ne mai amfani a rayuwa ta kuma wanda nake so, fatan kawai mutane za su dafawa abun domin ganin an kai ga gaci”. A cewar Klopp.

Liverpool ita ce dai a kan gaba da maki 25 wanda idan ta lashe gasar wannan dai shi ne karo na farko tun cikin shekaru 30 ba ta lashe gasar ba.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Za a ci kasuwanni a ranar da a ka bude Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada dama ga ‘yan kasuwar jihar Kano da su bude dukannin kasuwannin su a ranakun da a ka bude jihar Kano.

Kwamishin yada labarai na jihar, Kwamrade Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan cewa tuni gwamnati ta baiwa ‘yan kasuwar dama bayan ganawa da su ka yi da gwamnati.

‘Yan kasuwar za su bude kasuwannin na su ne tun bayan cikin tsawon kwanaki sama da 50 a rufe sakamakon bullar cutar Corona a jihar Kano.

Da dama dai wasu daga cikin ‘yan kasuwan sun ci kasuwar su a bayan fage musamman ma wasu daga cikin ‘yan kasuwar Kantin Kwari yadda su ka rinka yin kasuwanci irin samfurin tafi da gidan ka.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish