Connect with us

Manyan Labarai

Covid-19: Wata islamiyya ta gudanar da karatu a Kano

Published

on

Duk da gargadin da gwamnatin jihar Kano take na rufe makarantun jihar, an samu wata makarantar islamiyya mai suna Madarasatul Ta’alimuddeen mai dalibai kusan dari bakawai, a unguwar Dorayi karama dake karamar hukumar Gwale sun bude makarantar a safiyar yau Talata sun kuma gudanar da karatu.

A zantawar wakilin mu Abba Isah Muhammad da sakataren makarantar Sulaiman Ibrahim ya ce, “Muna koyi da fadar manzon Allah (S.A.W) idan abun alheri ya samu mumini ya godewa Allah, sai ya kara ninka masa alherin, yayin da sharri ya same shi ya koma ga Allah sai ya kawo masa tsari a ciki, sannan ya kawo masa mafita a cikin al’amarin”.

Ya kara da cewa, “A kullum mu dai muna cikin addu’a ne, domin mun mika al’amarin ga Allah, shi ya kawo mana cutar, kuma shi yasan yadda zai kawar mana ita, muna iya bakin kokari wajen rarraba yara a zaman da za su yi, da suturar da za su saka, da kuma irin abincin da za su ci”.

Ya kuma ce, “Mun ji labarin rufe makarantu, wasu an ce bangaren gwamnati, wasu kuma an ce gaba dayan islamiyyu, don haka sama-sama mu ka ji batun, bamu tabbatar da yadda al’amarin yake ba”. A cewar Sulaiman Ibrahim.

Malam Sulaiman Ibrahim ya nanata cewar, ba su samu wani mahaifi ya zo daukar dan saba saboda cutar Coronavirus, kullum ma kara turo yaran ake yi makaranta, kuma matakin da gwamnati ta dauka daidai ne amma mafita shi ne kawai a taru a roki Allah, fiye da rarrabuwar

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mun kammala shirin tunkarar aikin Hajjin bana -Muhammad Danbatta

Published

on

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Muhammad Abba Danbatta, ya ce, ya zuwa yanzu hukumar ta kammala shirin ta tsaf domin tunkarar al’amuran aikin hajjin bana.

Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala da safiyar yau Laraba.

Yana mai cewa, “Duba da wannan yanayi ake ciki na fama da annobar Coronavirus, ya sanya hukumar samar da sabbin tsare-tsare domin ganin an gudanar da aikin hajjin bana lafiya”.

Kazalika ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Kano ta kara kawo sabbin hanyoyin gwaje gwajen maniyyata domin tabbatar da lafiyar su kafin tafiya aikin hajji”. A cewar Muhammadu Danbatta.

 

 

Continue Reading

Labarai

Matasa sai sun rinka riko da sana’ar hannu -Isma’il Unique

Published

on

Wani kwararren mai sana’ar dinki a jihar Kano Isma’il Abdullahi Adam mai gidauniyar taimakawa marasa karfi ya ja hankalin matasa da su kasance masu dogaro da kai ta hanyar riko da sana’o’in hannu.

Isma’il Abdullahi ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Wannan Rayuwa na gidan rediyon Dala wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Kamata yayi idan mutum ya tashi ace ya san inda zai je domin gudanar da wata sana’a maimako zama yana jiran zuwan samun aikin gwamnati”.

Kazalika, kara da cewa, “Akwai sana’o’inmu na gado da ya kamata al’umma su rinka zamanantar da su, su bunkasa maimakon watsi da su”. A cewar Isma’il Abdullahi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnati sai ta kara tsaurara matakan shigowa Kano -Danbaito

Published

on

Wani Lauya mai zaman kansa a jihar Kano Barista Umar Usman Dan Baito, ya ce, kundin tsarin mulkin kasa sashi na 305, ya bawa Shugaban kasa damar da zai saka dokar ta baci a cikin kasar da yake mulki matukar hakan zai samar da mafita akan wani yanayi da kasar ta shiga.

Barista Dan Baito ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Shari’a a aikace na gidan Rediyon Dala, wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Dokar kasa ta kuma bayar da damar daukan mataki ga dukkanin mutumin da ya karya dokar da gwamnati ta sanya”. Inji Dan baito.

Dan Baito ya kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta kara tsaurara matakan tsaro kan dokar rufe iyakokin kano da aka yi, kasancewar duk da an rufe iyakokin, amma mutane suna cigaba da shigowa Kano ta barauniyar hanya daga wasu jahohinn kasar nan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish