Connect with us

Labarai

Covid-19 Kungiyar daliban Tukuntawa TUYODA ta raba sinadarin wanke hannu a masallatai

Published

on

Kungiyar daliban unguwar Tukuntawa TUYODA, da sauran hadin gwiwar kungiyoyin yankin sun dauki gabaran gudanar da rabon sinadarin wanke hannaye a cikin masallatan fadin yankin baki daya.

Kungiyar wadda ta fara daukan wannan matakin a cikin makon nan domin dakile yaduwar annobar cutar Covid-19 a yankin unguwar Tukuntawa dake karamar hukumar  birni da kewaye.

Sinadaren wanke hannuun da kungiyar TUYODA ta hada

Yayin rabon sinadarin wanke hannayen, Sakataren kungiyar, Zahradeen Usaini Lizarazu, ya ce ”Muna bin layi-layi na fadin unguwar domin wayar da kan al’umma cewa wannan cuta ta Coronavirus gaskiya ce domin haka muka gayyato mai hada magunguna ya kuma koya mana yadda a ke hada sinadarin wanke hannu, kuma muna bi masallatai da loko-loko na unguwar mu na rabawa domin kare kai”.

A nasa jawabin shugaban kungiyar TUYODA, Fardeen Aliyu, cewa ya yi” Muna wayar da kan mu ne kafin a ce wata kungiya ta zo ta taimaka mana daga waje, saboda haka mu ka hadu muka kirawo sauran kungiyoyin mu na cikin unguwa domin wayar da kan al’umma wajen wanke hannayen mu kafin mu ci abinci ko taba wani abu, domin haka muka kirawo guda daga cikin me hada magunguna ya koya mana muka kuma hada mu ke bi cikin masallatai domin raba wannan abun wanke hannun, harma mu bi inda majalisa take mu raba masu”.

Shi kuwa mai hada maganin, Pharmacist Auwal Bala, inda ya ce” A matsayi nan a mazaunin unguwar Tukuntawa mun zauna mun dauki wannan matakin ne domin hada wannan sinadarin wanke hannu kuma wanda kungiyar lafiya ta duniya ta amince da shi, domin ita ta bayyana yadda zamu hada shi cikin sauki wanda mutum zai iya hadawa a gida kuma ga shi da kudi kadan muka hada saboda wancan ya yi tsada, saboda haka muke kira da masu hannu da shuni da sauran al’umma da su tashi tsaye wajen bada tallafi ga irin wadannan kungiyoyi domin su hada su kuma rabawa al’umma”.

Guda daga cikin wanda suka rabauta da sinadarin wanke hannun’ Rabi’u Abdullahi Abubakar Tukuntawa ya ce” Sai dai mu yi godiya ga wannan kungiya sakamakon dama mu bamu dashi sai dai mu wanke hannu da ruwan kumfa kuma tabbas mun ji dadin wannan batu na wayar da kai da TUYODA take yi a Tukuntawa” A cewar mazaunin unguwar.

Labarai

Mai horas da kungiyar Southampton ya kara rattaba sabon kwantiragi

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Southampton, Ralph Hasenhuttl ya kara rattaba sabon kwantiragi a kungiyar ta Southampton.

Ralph Hasenhuttl mai shekaru 52 dan kasar Austrian ya karbi kungiyar ne tun a watan Disamba na shekarar 2018 wanda ya tsallake da su fadawa zuwa ajin ‘yan dagaji.

Mai horaswar ya dai rattaba sabon kwantiragi na tsawon shekaru hudu wanda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024.

Southampton dai ita ce kungiya da ta taba kwasar kashin ta a hannu har tsawon kwallaye tara da a ka zura mata a raga a gasar wanda Leicester City ta lallasa ta.

Continue Reading

Labarai

Naji dadi matuka da za a dawo gasar Premier -Mai horas da Liverpool

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce ya ji dadi sakamakon dawowa da za a yi gasar Firimiya a ranar 17 ga watan Yunin nan.

Klopp ya tabbatar da hakan ne ayayin tattaunawar sa da gidan rediyon BBC ya na mai cewa ya yi kewar wasan sakamakon hutun da a ka tafi na dakatar da wasan a ranar 13 ga watan Maris.

Ya ce” Na yi rashi sosai wannan abun mamaki ne domin kuwa abu ne mai amfani a rayuwa ta kuma wanda nake so, fatan kawai mutane za su dafawa abun domin ganin an kai ga gaci”. A cewar Klopp.

Liverpool ita ce dai a kan gaba da maki 25 wanda idan ta lashe gasar wannan dai shi ne karo na farko tun cikin shekaru 30 ba ta lashe gasar ba.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Za a ci kasuwanni a ranar da a ka bude Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada dama ga ‘yan kasuwar jihar Kano da su bude dukannin kasuwannin su a ranakun da a ka bude jihar Kano.

Kwamishin yada labarai na jihar, Kwamrade Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan cewa tuni gwamnati ta baiwa ‘yan kasuwar dama bayan ganawa da su ka yi da gwamnati.

‘Yan kasuwar za su bude kasuwannin na su ne tun bayan cikin tsawon kwanaki sama da 50 a rufe sakamakon bullar cutar Corona a jihar Kano.

Da dama dai wasu daga cikin ‘yan kasuwan sun ci kasuwar su a bayan fage musamman ma wasu daga cikin ‘yan kasuwar Kantin Kwari yadda su ka rinka yin kasuwanci irin samfurin tafi da gidan ka.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish