Connect with us

Labarai

Covid-19: Al’umma sun fara ganewa cutar ba wasa ba ce –Dr Sani

Published

on

Wani babban ma’aikacin banki a jihar Kano, Dr Sani Yahaya, wanda yake kula da shiyar Arewa maso Yamma, ya ce yanzu mutane sun fara ganewa cewa cutar Coronavirus ba wasa ba ce sai dai kawai al’umma su kara zage dantse wajen kula da matakan kariya.

Dr Sani Yahaya, ya bayyana hakan ne a lokacin da mu ke ganawa da shi dangane da batun samar da sinadarin wanke hannu a wajen injin cirar kudi na ATM tare da cinkoson da a ke yi a bankuna wajen cirewa da kuma ajiye kudi a Kano.

Ya ce”Da farko mutane sun dauki wannan cutar kamar wasa sakamakon idan mutum zai shiga banki idan an ba shi sinadarin wanke hannu su kan bijire su ki wanke, mu kuma sai mu hana mutum shiga cikin banki, kuma sai dai a yanzu ne wasu su ka gane cewa akwai cutar sakamakon yadda take kara ta’azzara a Nijeriya baki daya”.

“irin matakan da muka dauka a banki mu kan samar da kujeru mu bada tazara sosai a tsakanin mutane, domin ganin ba mu hada cinkoso ba gudun kamuwa da cutar Covid-19 tsakanin al’umma, kuma kasan mu’amala da kudi dole duk bayan minti shabiyar sai an wanke hannu da sinadarin wanke hannu, sannan kuma mu kan goge injin ATM sakamakon mu’amala da al’umma ke yi tun da ita cutar ba ganin ta a ke yi ba, kawai dai kira nag a al’ummar Kano su kara bada himma wajen rage cinkoso da yawan wanke hannu a duk inda su ke domin gudun kamuwa da cutar Coronavirus”. Inji Dr Sani.

Tun dai bayan shigowar cutar Coronavirus al’umma ke fargabar cewa wurin injin cirar kudi na daya daga cikin wuraren da bankuna a jihar Kano za su kara taka tsantsan domin kaucewa kamuwa da cutar a Kano da ma kasa baki daya.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending