Connect with us

Labarai

Covid-19: Yadda Kano ta kasance a yau

Published

on

Yanzu haka dokar hana zirga-zirga a jihar Kano ta kankama sakamakon yadda al’umma su ka bi umarnin gwamnati domin dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin Kano da ma kasa baki daya.

Cikin manya da kananun tituna na jihar Kano ya kasance babu ababan hawa a ko ina, sai dai idan ka ga giftawar mota ko babur walau na jami’an tsaro ne ko na jami’an asibiti ko kuma ‘yan jaridu masu neman labarai.

Wani bangaren titin Kano yadda a ka rufe shaguna

Haka zalika dukannin gidajen mai na Kano baki daya sun kasance a kulle a yayin da shagunan siyar da kayayyakin masarufi da manyan shaguna dukannin su suma a garkame su ke.

Wani gidan mai a Kano

Ha’ila yau dukannin kafafuwa sun tsaya cak sai dai daidai ku wadanda su ke kokarin zuwa wani bangare daga cikin yankin su ko kuma masu zama a bakin titi tare da kananan yara a kan titi.

Yara na guje-guje a kan titi

Wasu titunan kuwa irin su mahadar Dan Agundi da sauran su sun kasance an toshe wasu hanyoyin da sauran su wadanda ba za a iya shigewa ta hanyoyin ba.

A bangaren masu sana’ar siyar da shayi wajen ya kasance tamkar an yi shara, alamun cewa kamar jama’a ba su taba haduwa ba a wurin.

Wurin sana’ar masu siyar da shayi

su ma wuraren da a ke gudanar da sana’ar yin faci da kanikanci da sauran wurare sun kasance wurin babu kowa sai dai kayayyakin sana’ar su.

Bangaren masu yin faci

Idan kuwa mu ka duba ta bangaren kamfaninuka ba abun da za ka iske sai dai fankon gini kawai domin kuwa ko me gadi ba z aka gani ba a bakin wurin.

Yadda a ka garkame kamfaninuka

Da fatan al’umma za su ci gaba da bin umarnin gwamnati na za ma a cikin gidajen su domin ganin an dakile cutar Covid-19 a fadin Kano da ma kasa baki daya.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending