Connect with us

Labarai

Covid-19: Gwamnati ta kara kaimi wajen taimakawa al’umma -Sarkin Kano

Published

on

Maimartaba Sarkin Kano, Dr Aminu Ado Bayero, ya ce wannan doka da gwamnati ta dauka an dauke ta ne bisa shawarwarin masana lafiya domin dakile yaduwar ta a tsakankanin al’umma baki daya.

A cikin jawabin san a yau juma’a a kan cutar Coronavirus da ya yi, Dr Aminu Ado Bayero ya ce a wannan gabar ya ke kara baiwa al’umma su ci gaba da hakuri na halin da a ka tsinci kai a wannan rana.

Ya ce” Mu zama masu biyayya a kan wannan umarnin na gwamnati domin kasancewa a gidajen mu domin gudanar da ibadun mu a wannan rana ta juma’a da sauran ranaku domin kaucewa yaduwa daga wannan annoba, saboda haka ina kira ga dukannin jama’a mu jure da wannan al’amari da Allah ya jarabce mu da ita, mu bi shawarar masana mu yi biyayya ga dokokin gwamnati kamar yadda addinin mu ya tanada, mu tsananta neman tuba da kariya a wurin Allah, jama’a mu na jimame kwarai da gaske bisa halin da za a shi ga bisa yadda hana zirga-zirga za ta shafi harkokin neman abincin su da kuma nay au da kullum”.

Ya kuma ce“ Gwamnati da ta kara kaimi wajen fito da hanyoyin da za a taimakawa masu rauni da masu kananan sana’o’i da wannan dokar za ta fi shafa, mu na kuma sake kira ga dukan jama’a da mu yi azama mu amfana da wannan dama domin taimakawa ‘yan uwa da makwabta da sauran mabukata na kusa damu, lallai musulmi dan uwan musulmi ne, domin haka mu yi kokari mu tallafawa ‘yan uwan mu makwabtan mu da dukan mabukata tun kafin tsare-tsaren hukuma ya sadu ga kowa, mu na fatan gwamnati za ta gaggauta a wannan bigiren, yin hakan Allah madaukakin sarki zai sauko mana da rahamar sa da gaggawa, a karshe ina kira ga jama’a da su fahimci cewa duk kaddarar da ubangiji ya daurawa bayin sa, lallai za ta wuce idan a ka yi hakuri da juriya a ka koma gareshi a cikin tuba da tawali’u a ka kuma dai na sabawa dokokin sa, sannan kuma a ka bi shawarar masana”.  A jawabin sarkin Kano, Dr Aminu Ado Bayero.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending