Connect with us

Labarai

Covid-19: Idan ba a taimakawa talaka ba yunwa za ta yi masa illa -Kwamrade Babban Wano

Published

on

Kwamrade Auwal Rabi’u Babban Wando malami ne a sashen nazarin hallayar dan Adam kuma masani a fannin dake kwalejin Sa’adatu Rimi, ya ce akwai bukatar kulawa sosai ga al’umma musamman ma lokacin da a ke tunkarar azumi.

Cikin wata ganarwa sa Dala FM ya ce dole ne sai masu kudi sun fito da kudaden su domin tallafawa talakawa a wannan kullan da a ka yiwa al’umma.

Ya ce” Gwamnato ci su fito su yi gyara a kasafin da suka yi na rage kudade domin rabawa ga al’umma a wajen siyan kayan abinci, domin kuwa yin titi babu batun a yanzu, sakamakon a yau abinci talaka ya ke bukata. Kuma idan a ka ki taimakawa akwai matsala na yunwa kuma daga nan sai a mutu”.

Kuma “Gwamnati ki yi amfani da wannan halin na bin gida-gida ki na raba abinci, sannan idan za a yi kar a saka siyasa a ciki, kuma ‘yan adawa na siyasa duka ku fito ku bada tallafin ku da ministoci da dukannin masu rike da madafin iko a kasar nan, kuma har masu kudi su fito su rabawa talaka abinci, domin kuwa akwai matsala babba idan ba a baiwa talaka abinci ba a wannan halin da a ke ciki na killace al’umma”. Inji Babban wando.

Sannan ya kuma yi addu’ar wucewa lafiya daga wannan annobar mai sarkake numfashi ta Coronavirus.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending