Connect with us

Labarai

Covid-19: Gidauniyar Gharu Hira ta raba kayayyakin abinci ga marayu  

Published

on

Gidauniyar Gharu Hira Foundation dake unguwar Tukuntawa a karamar hukumar birni a jihar Kano, ta raba kayayyakin abinci ga marasa karfi dake yankin unguwar ta Tukuntawa.

Rabon kayayyakin abincin an yi shi ne a masallacin juma’a na Kuba dake yankin a yau Asabar.

Shugaban kungiyar, Adam Musa Dan Azumi Tukuntawa, ya ce” Ganin yadda mutane dake cikin ukuba ya sanya mu ka a ba su kayayyakin a cikin wannan lokacin da kowa yake da bukata. Sannan akwai kuma kayan sallah na mutum dari hudu a yanzu da za a ba su a nan gaba idan mun gama dinkawa maza da mata, duk marayun ne a ke ba su wanda duka mu ka sami tallafin ne daga Shehu Ibrahim Khalil wanda a ka fi sa ni da Baban Raga mazaunin unguwar Tukuntawa, shi ne ya bada wannan kayan abincin”. Inji Adam Tukuntawa.

Iayaye maya lokacin da su ke jiran karbar tallafin kayan abincin a cikin masallacin juma’a na Kuba dake Tukunta.

Gidanauniyar ta kuma bayyana cewa, mutum hamsim da bakwai ne wanda a ke ba su tallafin Makaroni da Taliyar ‘yan yara a duk shekara, amma a bana matasatsin ya yi yawa, kuma ga su iyayen marayu ne da ba su da wani mataimaki sai Allah.

 

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending