Labarai
Covid-19: Masu Corona sun haura 400 a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa mutane 427 ne su ka kamu da cutar Covid-19 a jihar.
Ma’aikatar lafiya ta Kano ta sanar a shafinta na Twitter cewa a ranar Laraba an samu karin mutane 30 da suka kamu da cutar a jihar.
Har ila yau, ma’aikatar lafiyar ta Kano ta ce an samu karin mutane 3 da a ka sallama bayan sun warke daga cutar, yanzu haka mutane 6 ne suka warke daga Coronavirus a jihar Kano.
Sanarwar ma’aikatar lafiya ta ce an samu karin mutane 5 da su ka rasa ransu sanadiyyar cutar ta Corona, wanda ya kai adadin wadanda cutar ta hallaka a jihar zuwa mutane 13.
Yanzu haka dai mutane 408 ne ke dauke da cutar wadanda su ke karbar kulawa daga wurin jami’an lafiya.
Jihar Kano dai ita ce jiha ta biyu a jihohin dake da yawan wadanda su ka kamu da cutar ta Covid-19 a kasar nan.
Ko a ranar Talata an tabbatar da cewa likitoci 34 ne suka kamu da cutar ta Covid-19 a jihar ta Kano.
Yayin da a ranar Laraba kuma rahotonni su ka tabbatar da cewa ma’aikatan jinya da Ungozoma 18 ne su ka kamu da cutar ta Covid-19 a Kano.
Labarai
Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge
Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.
Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.
A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.
Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.
Labarai
Ku guji tada hankalin al’umma yayin zaɓen ƙananan hukumomi a Kano – Human Right
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta buƙaci al’umma musamman ma Matasa da su kasance masu bin doka da oda tare kuma da gujewa tayar da hankalin jama’a a yayin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin da za ayi a yau Asabar.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar na Ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a safiyar Asabar.
Ya kuma ce bai kamata al’umma su kasance masu taka doka ba, domin bin doka shi ne wayewa.
“Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su bada gudunmawar su yayin zaɓen domin ganin an gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin cikin kwanciyar hankali, “in ji Tasi’u”.
Da yake nasa jawabin daraktan ƙungiyar Kwamared Gambo Madaki, kira ya yi ga dukkanin ƴan ƙungiyar su na ƙananan hukumomin Kano 44, da ku guji sanya kayan ƙungiyar su yayin gudanar da zaɓen kasancewar ba sa cikin masu aikin zaɓen ko kuma sanya ido, domin gujewa fuskantar matsala.
Tuni dai hukumar zaɓe ta jihar Kano Kanseic, ta ce za’a fara kaɗa ƙuri’a ne da misalin ƙarfe takwas na safiyar yau Asabar.
Labarai
Sarkin Kano ya ɗaga likkafar Alhaji Abbas Ɗalhatu daga Ƴan Daka, zuwa Bauran Kano, da naɗa hakimai 10
Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Alhaji Abbas Ɗalhatu shugaban rukunin gidajen Freedom Radio da Dala FM, a matsayin Bauran Kano, bayan da ya ɗaga likkafar sa daga Ƴan Ɗakan Kano.
Sarkin ya naɗa hakiman ne da safiyar yau Juma’a, inda ya kuma naɗa hakimai goma a matakai daban-daban, daga cikin su akwai Kacallan Kano, da Dan Adalan Kano, da mai unguwar Munduɓawa kuma hakimin Gezawa, da sauransu.
Da yake jawabi jim kaɗan da ɗin hakiman da kuma ɗaga likkar Alhaji Abbas Ɗalhatu zuwa Bauran Kano, mai martaba Sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce an naɗa hakiman ne bisa jajirecewar su da taimaka wa al’umma da kuma biyayya ga masarautar Kano.
Sarkin na Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya kuma hori dukkanin hakiman da su mayar da hankali akan samar da ci gaban al’ummar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Wakilinmu Yakubu Ibrahim Doragarai ya ruwaito cewa a yayin naɗin al’umma da dama ne suka samu damar halarta daga ciki da wajen ƙasar nan.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su