Connect with us

Labarai

Marayu 324 su ka samu kayan sallah a unguwar Tukuntawa

Published

on

Cibiyar tallafawa marayu na Masjid Kuba dake unguwar Tukuntawa a karamar hukumar birni a jihar Kano, ta rabawa marayu maza da mata kimanin 324 kayan sallah dake fadin yankin.

Rabon kayan sallah ga marayun ya gudana a harabar masallacin Juma’a na unguwar Tukuntawa.

Shugaban kungiyar, Adam Musa Dan Azumi ke jawabi a yayin taron.

Shugaban kungiyar, Adam Musa Dan Azumi, ya ce” Wannan dai shi ne kashi na shida da mu ka yi rabon kayan wato yau shekaru shida kenan mu na yi, mun raba kayan sallah na marayu su mutum 324 a tsakanin maza da mata wanda mu ka gayyaci yaran da ba su wuce hamsin ba, saboda dokar hana taruwa da yawa, wannan shi ma mu na samun taimako ne daga daliban makarantar Gharu Hira bangaran matan aure da kuma wasu na waje kamar su Engr. Shehu Ibrahim Khalil Baban Raga da wasu da yawa da su ka bamu gudunmawa musammamma shi Engr ya dau nauyin yara mutum dari da saba’in mata dari da goma sha biyar sai ragowar maza, kuma taron ya sami hallartar dagacin unguwar Gandu da mai unguwar Tukuntawa da mai unguwar Kwandilar Gandu da shi kansa Engr. Ibrahim Khalil da sauran Malan makaranta karkashin shugabancin makarantar Mal Nura Umar Abdulaziz”. A cewar sa.

Cibiyar tallafawa marayu ta Gharu Hira ta kum Ja hankalin mawadata da su fito su taimaka a irin wannan aikin sakamakon mawuyacin halin da marayu ke sha a rayuwar su.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending